Marigayiya A’isha ta kware sosai a aikin jarida da shirye-shiryen talabijin.
Kafin rasuwarta, Aisha ta rike mukamin babbar manaja a bangaren shirin Majalisa na gidan talabijin na NTA, bayan ta shafe shekaru 30 a matsayin mai gabatar da labarai.
Aisha ta fara aiki a NTA a matsayin mai daukowa da rubuta labarai, har ta kai matsayin mataimakiyar darakta a fannin labarai, sannan ta zama babbar manaja a fannin shirin 'yan majalisa na NTA. Aisha ta kasance daya daga cikin fitattun masu watsa shirye-shirye a NTA a daga shekarar aluf dari tara zuwa farkon shekara ta 2022 lokacin da ta yi ritaya.
Marigayiya Aisha Bello ta yi fice a matsayin matan arewacin Najeriya na farko da suka fara karanta labaran duniya da turanci a tashar talabijin ta kasa NTA, ta kuma zama abin koyi da alfahari ga matasan arewacin kasar da dama musamman 'yan jarida mata.
A wata sanarwa da ke dauke da sa hannun wani hadimin Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, Ajuri Ngelale, Shugaban kasar, ya bayyana Aisha a matsayin abin koyi da kuma alfahari ga mata. Shugaba Tinubu ya ce za a ci gaba da tunawa da yaba aikin da ta yi, yayinda ya kuma jajintawa 'ya'ya da iyalin da ta bari a baya.
Wakazalika ma'aikatar watsa labarai ta Najeriya ta wallafa sanarwar rasuwar tsohuwar 'yar jaridar da jajen shugaban kasa a shafinta na sada zumunta X.
Wadansu matasa sun bayyana jimamin rasuwar tsohuwar 'yar jarida a dandalin sada zumunta na X.
Marigayiya Aisha ta yi aiki na tsawon shekaru da dama da fitattaccen mai gabatar da labarai a tashar talabijin ta kasa NTA, Cyril Stober wanda ya yi ritaya a shekarar 2019.
Aisha ta sami horo a fannin aikin jarida a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zari'a, inda ta sami digiri na farko a fannin harkokin sadarwa.
Dandalin Mu Tattauna