Dan wasan Najeriyan da ya yi fice a kungiyar Napoli a gasar Seria A Victor Osimhen, ya lashe kyautar lambar yabo ta CAF na shekarar 2023, wanda hukumar kwallon kafar Afirka ta shirya, yayin karrama ‘yan wasa da ya gudana a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba a birnin Marrakech na kasar Morocco.
A kakar wasan da ta kare dai, Osimhen mai shekaru 24 ya ci kwallaye 31, wadanda suka taimaka wa kungiyarsa ta Napoli lashe kofin gasar Seria-A karo na farko cikin shekaru 33. Ya kuma sheke tarihin Samuel Eto’o na Kamaru na wanda ya fi yawan cin kwallaye a cikin 'yan wasan Afirka.
Osimhen ya yi takara tare da dan wasan Morocco Achraf Hakimi da na Masar Mohamed Salah.
Dan wasan shi ne ya kai Super Eagles gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a badi, wanda ya ci kwallo 10 a karawar cancantar shiga gasar.
Dan wasan ya kuma kafa tarihin zama dan nahiyar Afirka da ke kan gaba wajen cin kwallaye mafiya yawa a gasar Seria A da adadin kwallayen 26, kambin da a baya tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya George Weah ne ke rike da shi a babbar gasar kwallon kafar ta kasar Italiya.
Osimhen kuma shine dan Najeriya na farko da ya lashe kyautar tun bayan Nwankwo Kanu a shekarar 1999.
A fannin mata kuma Asisat Oshoala (Najeriya, Barcelona) ita ce ta lashe gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2023.
Ta kuma yi takara tareda Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu, Racing Louisville) da kuma Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli).
Dandalin Mu Tattauna