Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Sha Alwashin Daukaka Kara Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Na Hana Shi Takara


Tsohon Shugaban Amurkal Donald Trump
Tsohon Shugaban Amurkal Donald Trump

"Kotun koli ta Colorado ta fitar da wani hukunci mai cike da kura-kurai a daren yau kuma za mu shigar da kara cikin gaggawa zuwa kotun kolin Amurka." in ji mai magana da yawun yakin neman zaben Trump

Kotun kolin jihar ta yanke hukuncin dakatar da tsohon shugaban kasar Donald Trump daga zama shugaban kasar Amurka, kuma ba zai iya fitowa a zaben fidda gwani a jihar Colorado ba, saboda rawar da ya taka a harin da magoya bayansa suka kai Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Jana'irun 2021.

Kotun, wadda alkalanta hudu bisa uku suka amince da hukuncin, zai sa Trump ya zama dan takarar shugaban kasa na farko da ake ganin bai cancanci shiga fadar White House ba a karkashin wani tanadin kundin tsarin mulki da ke haramtawa jami’an da suke tada kayar baya ko yin bore ga hukumomi" daga rike mukami.

Trump Capitol Riot
Trump Capitol Riot

Hukuncin ya nuna cewa Mr. Trump bai cancanta tsayawa a matsayin dan takara ba, saboda ya sanya an yi zanga-zanga a majalisar dokokin Amurka, kusan shekara uku da suka wuce.

Mr Trump zai iya tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa, sai dai hukuncin zai kara haifar masa da sarkakiya.

Hukuncin na magana ne kadai a kan zaben fidda gwanin da za a yi a jihar a ranar 5 ga watan Maris din shekara mai zuwa, lokacin da jam'iyyar Republican za ta zabi wanda zai tsaya mata takarar shugabancin kasa.

Kotun Colorado
Kotun Colorado

Sai dai hakan zai shafi babban zaben da za a yi a watan Nuwambar shekarar ta 2024.

Wannan ne karon farko da aka yi amfani da sashe na uku na kudin tsarin mulkin da aka yiwa gyaran fuska na 14, wajen hana dan takarar shugaban kasa tsayawa.

Hukuncin na ranar Talata wadda ba za a yi aiki da shi ba tukuna har sai an daukaka kara a watan gobe, ya shafi jihar ta Colorado ne kadai.

Hukuncin da alkalan suka rubuta ya ce:

"Cimma wannan matsayi ba abu ne da ya zo mana da sauki ba. Muna sane da irin girma da nauyin tambayoyin da za mu fuskanta.

"Hakazalika muna sane da girman rantsuwar da muka yi na yin aiki da doka ba sani ba sabo kuma ba tare da mun bar ra'ayoyin jama'a sun yi tasiri a kanmu ba, kan hukuncin da ya zama dole mu cimma."

Kotun ta dage yanke hukuncin har sai ranar 4 ga watan Janairu, ko kuma har sai kotun kolin Amurka ta yanke hukunci kan karar. Jami'an jihar Colorado sun ce dole ne a warware batun nan zuwa ranar 5 ga watan Janairu, wa'adin da jihar ta bata na buga kuri'un zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Mai magana da yawun yakin neman zaben Trump ya ce:

"Kotun koli ta Colorado ta fitar da wani hukunci mai cike da kura-kurai a daren yau kuma za mu shigar da kara cikin gaggawa zuwa kotun kolin Amurka."

Trump ya rasa Colorado da maki 13 a 2020 kuma ba ya bukatar jihar domin lashe zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG