Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt goma a kogunan Otamiri da kuma Nworie da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.
An bukaci majalisun dokokin Najeriya da su kirkiro tsarin dokar gine-gine don shawo kan matsalar rushewar gidaje da ake yawan gani a sassan kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake kai ziyara Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ta kammala, duk da barazanar 'yan aware.
Yayin da bangarori daban daban na hukumomin Najeriya ke kintsawa don tinkarar babban zaben Najeriya na 2023, su ma 'yan sanda ba a bar su a baya ba.
Yayin da hukumomi na ci gaba da inganta dabaru wajen samar da maslaha ga matsalar tsaro da kasar ke fama da ita, ‘yan sanda dai a jihar Kros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ce suna samun gagarumar nasara akan miyagun laifuka a fadin jihar.
Malaman jami’a a kudu maso gabashin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan zanga-zangar wuni biyu da kungiyar kwadago zata fara gudanarwa yau Talata don bai wa malaman jami’a hadin kai a yajin aikin da su ka kwashe kimanin wata shida suna yi kan gazawar gwamnatin wajen mutunta yarjejeniyarsu.
Mazauna kasuwar shanu ta Lokpanta da ke garin Umuchieze a jihar Abia, galibi matasa, sun gudanar da zanga-zanga da safiyar jiya Asabar don bayyana fushinsu kan kashe wani makiyayin da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka yi a dajin wani kauyen garin.
An yi jana’izar shahararriyar mawakiyar bishara Osinachi Nwachukwu jiya a garin Isuochi da ke jihar Abia, inda daruruwan jama’a suka taru domin yi mata girmamawar karshe.
Wata kotu a Birtaniya ta hana belin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu da uwargidansa, bayan an gurfanar da su bisa zargin kulla makarkashiyar safarar wani yaro zuwa Birtaniya domin girbe wani sashin jikinsa.
Al’ummar kudu maso gabashin Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan zabin da ‘yan takaran shugaban kasa na jam’iyyan PDP da Labour Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi, na daukar gwamnan jihar Delta Sanata Ifeanyi Okowa da Dakta Doyin Okupe a matsayin mataimakan takara a zaben da za a gudanar.
Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar Labor yana daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa masu karancin shekaru a jerin 'yan takarar shugaban kasa na 2023.
Wata babbar kotu a jihar Abia ta soke zaban Cif Ikechi Emenike a matsayin dan takaran gwamnan jihar Abia na jam'iyar APC a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Alhamis.
Wannan shi ne karo na uku da Shugaba Buhari yake kai ziyara jihar ta Ebonyi, na farko a watan Nuwamban shekarar 2017, na biyu kuma a watan Janairun shekarar 2019.
Wasu mutune biyu sun mutu a fashewar bam da ta auku a kamfanin man Addax da ke garin Izombe na karamar hukumar Oguta ta jihar Imo a safiyar jiya Laraba, kimanin kwanaki goma bayan wata fashewa ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 100 a wata matatar mai a jihar Imon.
Iyalai, 'yan'uwa da dangi na ci gaba da jimamin akalla mutum 100 da suka mutu sakamakon wata fashewa da ta auku a wata haramtacciyar matatar mai da ke dajin Abaezi na karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo a daren Jumma'ar da ta gabata.
'Yan sanda a jihar Inugu sun ce sun cafke wata mata bisa zargin sace wani yaro mai shekaru 7 daga Zaria da ke jihar Kaduna, da aniyar sayar da shi a jihar Inugun, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Inugu Mista Daniel Ekea ya shaida.
Wuni guda bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari ofishin 'yan sanda a garin Atani inda suka hallaka ma'aikata hudu a safiyar ranar Laraba, rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta murkushe wani yunkurin kai hari shelkwatar 'yan sanda da ke garin Nteje a safiyar yau Alhamis.
An samu bambancin ra'ayi tsakanin gwamnatin jihar Anambra da ma'aikatan jihar kan batun umurnin da gwamnati ta bada cewar kowane ma'aikaci ya rika zuwa ofis a kowace ranar Litinin, duk da ci gaba da fuskantar barazana daga 'yan awaren Biafra.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa za ta tura karin ma'aikatan tsaro jihar Imo, don inganta yanayin tsaro a wannan jihar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da ma wasu tashin-tashinan.
Domin Kari