Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ganin Sakacin Gwamnati A Fashewar Da Ta Lakume Rayukan Mutane 100 A Imo


Fashewa a wata haramtacciyar matatar mai.
Fashewa a wata haramtacciyar matatar mai.

Iyalai, 'yan'uwa da dangi na ci gaba da jimamin akalla mutum 100 da suka mutu sakamakon wata fashewa da ta auku a wata haramtacciyar matatar mai da ke dajin Abaezi na karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo a daren Jumma'ar da ta gabata.

Ko da ya ke gwanatin Najeriya ta riga ta dora alhakin mutuwar wadannan mutane akan masu wannan haramtacciyar matatar mai, galibi, musamman masu fashin baki, na cewa sakaci da kuma gazawar gwamnati wajen samar wa al'umma abin yi ne ya sa ake tururuwa zuwa haramtattun matatun mai.

Haka kuma jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu akan wannan ibtila'in da ya fada wa al'ummar jihar.

Wani marubuci Dakta Amanze Obi ya bayyana cewa, "Abin takaici ne satar mai na faruwa a gaban hukumomin tilasta doka kuma basa komai game da ita, saboda duk an bata su. Kuma zaka tarar cewa galibi masu satar mai matasa ne da basu da aiki, kuma gwamnati bata tallafa musu, da yasa suke neman hanyar taimaka wa kansu. Abin da suke yi bai dace ba, amma halin da suka tsinci kansu ne yasa suke yi abin da bai dace ba, kuma hukumomi basa daukar mataki saboda suna daya daga cikin matsalolin da ke addabar kasar."

"Gazawar gwamnati wajen samar wa jama'a aiki ne ya janyo wannan. Kuma gazawar gwamnati wajen farfado da matatun man mu ya samar wa wasu haramtattun wuraren gudanar da harkokinsu," inji Dakta Osita Nwosu.

A nasa bayanin da Mista Maurice Ogbonna, wani dan asalin karamar hukumar Ohaji/Egbema, inda gobarar ta auku, ya bayyana cewa, "Gwamnati ta ki ta kula da su tun da dadewa. Shi ya sa matasan yankin ke fita suna neman hanyoyin raya kansu."

"Hanya kadai da za a iya daina irin wannan ta'adin ita ce gwamnati dauki matakai kwakkwara don tabbatar da cewa an samar wa akasarin matasanmu da ke kara zube abin yi, saboda idan suna da abin yi ba za su tsunduma cikin satar mai ba. Kuma idan muna da jami'an tilasta doka wadanda zasu tabbatar cewa ba'a jure wa irin wannan haramtaccen aiki ba, tabbas mutane zasu daina," inji Dakta Amanze Obi.

Yanzu rundunar 'yan sandan jihar Imo ta ce tana gudanar da bincike kan wannan gobarar, da zummar gano ainihin musabbabinta, yayin da gwamnatin Najeriya ta bada umurnin kama masu wannan haramtacciyar matatar mai.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG