Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Tarihin Peter Obi Dan Takaran Shugaban Kasa Na Jam’iyyar Labour


Peter Obi
Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyar Labor yana daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa masu karancin shekaru a jerin 'yan takarar shugaban kasa na 2023.

An haifi Mista Peter Obi a ranar 9 ga watan Yulin shekarar 1961 a garin Onitsha na jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.


Ilimi
Bayan ya kammala makarantar firamari, Obi ya halarci Christ the King College, inda ya kammala karantun sakandare. Daga nan ya samu shiga jami’ar Najeriya da ke garin Nsukka a shekarar 1980, inda ya samu digiri a ilmin Falsafa a shekarar 1984.

Daga nan kuma Obi ya halarci Lagos Business School a birnin Legas na Najeriya, da Harvard Business School da ke birnin Cambridge na Amurka, da London School of Economics na jami’ar Columbia da ke birnin New York a Amurka, da kuma Institute for Management Development da ke kasar Switzerland. Haka kuma, ya je Kellogg Graduate School of Management a Amurka, da Said Business School na jami’ar Oxford da ke kasar Ingila, da kuma Judge Business School na jami’ar Cambridge a kasar Ingila.

Sana'a

Kafin ya shiga siyasa, Obi dan kasuwa ne wanda ya rike mukamai da dama a wasu masana’antu masu zaman kansu, ciki har da Next International Nigeria Ltd, da Guardian Express Bank Plc, da Future View Securities Ltd, da Chams Nigeria Ltd, da Paymaster Nigeria Ltd, da kuma Fidelity Bank Plc.

Siyasa

A shekarar 2003, Obi ya shigo fagen siyasa a matsayin dan takaran gwamnan jihar Anambra na jam’iyyar APGA, inda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta ayyana dan takaran jam’iyyar PDP Chris Ngige a matsayin wanda ya lashe zaben, amma a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2006, kotun daukaka kara ta ayyana Obi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan.

An rantsar da Obi a matsayin gwamnan jihar Anambra a ranar 17 ga watan Maris shekarar 2006. Majalisar dokoki ta jihar Anambra ta tsige Obi daga gwamna a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2006, inda mataimakiyarsa Virginia Etiaba ta maye gurbinsa a matsayin gwamnar mace ta farko a tarihin Najeriya. Amma Obi ya kalubalanci tsige shi da majalisar jihar ta yi, kuma kotun daukaka kara ta dawo da shi kan kujerar gwamnan jihar Anambra a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2007.

Obi ya sake barin kujerar gwamna a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, biyo bayan zaben da aka gudanar, wanda dan takaran jam’iyyar PDP Andy Uba ya lashe. Amma Obi ya koma kotu da cewar bai kammala wa’adinsa na shekaru hudu ba, lamarin da ya sa kotun koli ta Najeriya ta dubi batun ta mayar da shi kan kujerar a ranar 14 ga watan Yunin shekarar 2007.

Obi ya nemi wa’adi na biyu a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a shekarar 2010, kuma a ranar 7 ga watan Fabrairu shekarar 2010, hukumar zabe ta kasa ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hoton 'yan takarar shugaban kasa na Jam'iyar PDP Atiku Abubakar a da abokin takararsa Peter Obi da aka kafa a wata hanyar birnin Abuja, Nigeria, Feb. 19, 2019.
Hoton 'yan takarar shugaban kasa na Jam'iyar PDP Atiku Abubakar a da abokin takararsa Peter Obi da aka kafa a wata hanyar birnin Abuja, Nigeria, Feb. 19, 2019.

Bayan kammala wa’adin mulki na biyu, Mista Peter Obi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kuma a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 2018, aka ayyana shi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar, inda suka zo na biyu a zaben shekarar 2019.

A ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2022, Obi ya ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin tutar PDP a zaben 2023. Amma ya canza sheka zuwa jam’iyyar Labour, inda aka ayyana shi a matsayin dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar a zaben fid da gwanin da aka gudanar a babban birnin jihar Delta na Asaba a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2022.

Mista Peter Obi mai shekaru 60 a duniya, ya auri Margaret Brownson a shekarar 1992, kuma suna da ‘ya’ya biyu.

Saurari cikakken tarihin cikin sauti:

Takaitaccen Tarihin Peter Obi Dan Takaran Shugaban Kasa Na Jam’iyyar Labour
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

XS
SM
MD
LG