Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Tura Karin Dakaru Zuwa Jihar Imo


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta  tabbatar da cewa za ta tura karin ma'aikatan tsaro jihar Imo, don inganta yanayin tsaro a wannan jihar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da ma wasu tashin-tashinan.

Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wasu a jihar Imon, musamman mazauna, suka bukaci gwamnatin tarayyar kasar ta yi maza ta hanzarta kokari wajen kawo musu dauki, saboda yadda matsalar tsaro ke matukar shafar wanzuwarsu da kuma lamuransu na yau da kullum.

Tuni gwamnatin jihar Imo ta yaba da wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, kamar yadda kwamishinan yada labarai Mista Declan Emelumba ya bayyana.

Ya ce, "Wannan zai taimaka wa gwamnatin jihar ta inganta tsaro a jihar, don gwamnati ta saje da duk wata barazanar da matsalar tsaron da muke fama da ita. Da wannan, gwamnati za ta iya tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a ko wane lokaci."

Shi kuwa Mista Chisom Martins Igboko na cewa, "Kamata tabarbarewar tsaro a jihar Imo a halin yanzu ya zama abin damuwa ga kowa. Kyakkyawan mataki ne gwamnati ta dauka na kara adadin ma'aikatan tsaro. Kuma ta haka za a iya tabbatar da tsaro a duk wuraren da ke fama da karancin ma'aikata a jihar,"

Shi kuwa Mista Maurice Okorie cewa ya yi, "idan har za su iya karya lagon masu haddasa fitina a jihar, toh kara ma'aikatan ya yi. Amma wani sa'in ana amfani ne da ma'aikata wajen razana jam'iyyun adawa da abokan hammaya, ganin cewa zabe na gabatowa."

Tun watan Afrilun bara ne lamura a jihar Imo suka rikice da hare-haren 'yan bindiga, kuma tun wannan lokacin ne hukumomi suke ta gwada dabaru da zummar maido da zaman lafiya a jihar Imon.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG