Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Biyu Sun Mutu Sanadiyar Fashewar Bom A Kamfanin Mai Da Ke Jihar Imo


Lokacin da ake binne mamatan a jihar Imo
Lokacin da ake binne mamatan a jihar Imo

Wasu mutune biyu sun mutu a fashewar bam da ta auku a kamfanin man Addax da ke garin Izombe na karamar hukumar Oguta ta jihar Imo a safiyar jiya Laraba, kimanin kwanaki goma bayan wata fashewa ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 100 a wata matatar mai a jihar Imon.

Koda ya ke 'yan garin Izombe da dama sun ki ce wa uffan akan wannan lamarin, Mista Gabriel Nwafor, shi ma dan asalin garin Izombe da kuma mazaunin garin, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, "Akwai matasa maza da suka je da nufin tada kamfanin, amma yayin da suke kokarin kutsa wa wurin sai bam din ya fashe ya kashe su. Tana yiwuwa sun karbi kudi ne daga wasu su cinna wa kamfanin wuta. Ka san wasu na iya aikata komai saboda kudi."

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta riga ta tabbatar da aukuwar wannan al'amarin.

Kamfanin Addax Petroleum yana daya daga cikin kamfanonin mai biyu da ke garin Izombe mai arzikin man fetur. Kuma wannan garin na daya daga cikin garuruwa masu fuskantar barazana sosai daga ayyukan 'yan bindiga a jihar Imo.

Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe cikin sauti:

Mutane 2 sun mutu a fashewar bom da ya auku a jihar Imo-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG