Har yanzu mazauna jihar Anambra na ci gaba da zaman zullumi sakamakon kashe wata mai suna Harira Jibril, 'yar Arewa 'yar asalin karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa mai juna biyu da 'ya'yanta hudu, da kuma wasu ‘yan Arewa.
ANAMBRA, NIGERIA - Kisan da wasu 'yan bindiga suka yi a ranar Lahadin da ta gabata, kimanin wuni guda kenan bayan wasu 'yan bindigan kuma suka fille kan wani dan majalisar dokokin jihar Anambra, Honarabul Okechukwu Okoye.
Wani Banufe mazaunin jihar mai suna Shehu Bagana ya ce yanzu haka abin da ke faruwa a jihar akwai ban tsoro.
Shi kuwa Muhammad Lawan Ibrahim Katsina ya ce yanayin rashin tsaron da mazauna suka tsinci kansu a ciki ya sa baki suna watsewa a halin yanzu.
Alhaji Yusha'u Imam Wazirin Hausawa a garin Anacha na jihar Anambra, ya ce duk da cewa hare-haren 'yan bindiga ba bakon abu ba ne, abin da ya faru a ranar Lahadin da ta wuce ya yi muni.
Ko da yake, yunkurin samun kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Anambra DSP Tochukwu Ikenga kan wannan lamarin ya ci tura, amma jaridar Pulse ta ruwaito cewa wasu matasa a karkashin tutar wata hadakar kungiyar shugabannin matasan yankin kudu maso gabas da ke kasar kabilar Igbo sun yi Allah wadai da wadannan kashe-kashen tare da kira ga gwamnatin jihar Anambra da ta yi maza ta kafa kungiyar tsaro ta matasa don kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a fadin jihar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Alphonsus Okoroigwe: