Yanzu dai a wannan yanki na kabilar Igbo, a yayin da wasu na ganin daukar Okowan da Atiku ya yi ya dace, wasu kuwa na cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP bata yi wa yankinsu wani adalci ba.
Dakta John Onoh wani malamin jami’a ne da ke ganin Atiku Abubakar ya nuna basira a daukar Ifeanyi Okowan da ya yi.
Ya ce, “Ifeanyi Okowa dan kabilar Igbo ne, amma kuma dan yankin kudu maso kudu ne. Saboda haka zai yi wuya mutum ya ce ba a dauki dan kabilar Igbo ba. Kuma zai wuya a ce ba a dauki dan yankin kudu maso kudu ba. Ni dai wannan zabin shine mafi alheri ga Atiku. Kuma kowane shugaban kasa na bukatar mataimaki mai rikon amana.”
Sai dai Mista Chisom Martins ya fadi cewa duk da cewa Ifeanyi Okowa ya cancanta a matsayin mataimakin takara, da daukar mataimaki daga kudu maso gabas ya fi dacewa.
“Ifeanyi Okowa dan takara ne mai inganci, idan aka yi la’akari da tarihinsa da kuma dabi’arsa. Amma duk da haka, idan har daidaito da adalci ake yi, zan ce da daukar mataimaki daga kudu maso gabas ya fi. Akalla, da ya huce zafin fafutukar da ake yi a yankin Igbo,” inji Chisom Martins.
Ko da ya ke Dakta Doyin Okupen da jam’iyyar Labour ta dauka a matsayin mataimakin takaran Peter Obi ya ce zaman wucin gadi ne ya ke yi, Injiniya Emmanuel Agbo na ganin ya kamata Peter Obi ya tabbatar cewa duk wanda zasu dauka a wannan matsayin ya kasance mutum ne mai farin jini wanda zai samu karbuwa a fadin kasar.
Emmanuel ya kara da cewa, “Okupe dan siyasa ne mai kyau kuma mun san shi wani jigo a Najeriya. Amma ina tunanin zasu fi samun shiga idan suka dauki dan arewa.”
Tuni kungiyar kare muradun kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta riga ta taya gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa murnar daukarsa da dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi, amma ta ce yanzu tana nazari ne kan yadda ‘yan kabilar Igbo zasu kada kuri’unsu.
Inji kakakin kungiyar Dakta Alex Ogbonnia, “Kungiyar Ohanaeze Ndigbo tana nan tana kallon yadda ake zaban ‘yan takaran shugaban kasa da mataimakan nasu, kuma ana sa ran cewa ba da jimawa ba zamu zauna da duk masu ruwa da tsaki na yankinmu mu yanke shawara kan yadda zamu yi zaben shekarar 2023.”
Saurari cikakken rahaton cikin sauti: