ABIA, NIGERIA - Matasan dai sun fantsama ne daruruwansu a kan babban titin Inugu zuwa Fatakwal inda suka yi zaman dirshan suna kona tayoyi tare da kokawa kan wannan danyen aikin, lamarin da ya tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a kan titin na tsawon sa’o’i da dama.
Wani ganau, Alhaji Magaji Dede, ya shaida wa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru inda ya kara da cewa akalla shanu goma ne maharan suka kashe a dajin kauyen.
Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar shanun, Alhaji Awwal Hamman, ya yi karin haske tare da cewa hukuma ta riga ta shigo cikin lamarin a yayin da kura ke ci gaba da lafawa.
To sai dai dama bata samu ba wajen tabbatar da aukuwar wannan lamarin daga bangaren hukuma, saboda duk yunkurin samun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abia, Mista Geoffrey Ogbonnaya ta wayar tarho, ya ci tura.
Saurari rahoton daga Alphonsus Okoroigwe: