Rundunar ‘yan sandan birnin Landan sun cafke Ike Ekweremadu da matarsa ne a Landan biyo bayan wani binciken da tawagar kwararrun masu binciken manyan laifuka ta gudanar, kuma ta bada wasu karin bayanai da cewa bayanan da aka bada sun zo daidai da bayanai kan Ekweremadu da matarsa.
Yanzu yayin da wannan lamarin ke ci gaba da daukar hankali a fadin Najeriya, jama’a da dama kuwa sai bayyana ra’ayinsu su ke yi, ciki har da Mista Igboko Chisom, wanda kafin a gurfanar da sanatan da matarsa ya fadi cewa “Ina so in yi imani da cewa akwai sabani a wani wurin, saboda bana sa ran cewa sanatan zai tsoma hannu cikin harkar girbe sashin jikin mutum. Amma kuma bana so in ce ‘yan sandan Birtaniya zasu iya zargin sanatan da aikata irin wannan laifin ba tare da wata hujja ba.”
Mista Emeka Onah wani mai fashin baki ne kan lamuran siyasa, kuma yana ganin wannan al’amarin a matsayin wani mumunan lamari ga sanatan. Ya bayyana cewa, “Wannan ba wani lamari bane mai kyau ga wanda ya kai wannan matsayin a siyasance. Saboda haka, ya kamata ya fuskanci kuliya.”
Shi kuwa Dakta Okechukwu Nwosu ya bayyana bacin rai da irin ‘yan siyasan da suka mamaye kujerun mulki a kasar. “Wannan na gaya maka halayyar ‘yan siyasan da muke da su a Najeriya. Wannan na gaya maka cewa muna da mutanen da basu da halayya ta kwarai, wadanda basu cancanci su kasance a kujerun mulki ba. Wannan abin takaici ne. Amma bari mu ga yadda za a gama a kotu,” inji Dakta Nwosu.
Yanzu Ekweremadu da matarsa zasu ci gaba da kasancewa a tsare har sai sun sake gurfana gaban kuliya a ranar 7 ga watan Yuli mai zuwa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: