Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Malam Aminu Alhassan ne ya shaida wa Muryar Amurka hakan a wata hira, inda ya karkare da cewa kalubalolin da ‘yan sanda ke fuskanta a jihar yanzu ‘yan kalilan ne, kamar batun ayyukan masu fafutukar kafa kasashen Biafra da Ambazonia, da kuma batun masu safarar makamai.
Sai dai Malam Musa Kutama wani mai fashin baki kan lamuran yau da kullum da kuma mazaunin Calabar, babban birnin jihar Kros Riban, ya ce duk da cewa ana samun nasarar, har yanzu akwai bukatar kara inganta tsaro a wuraren shakatawa da makarantu da wuraren kasuwanci, da kuma sauran wuraren walwala.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: