ANAMBRA, NIGERIA - A 'yan kwanakin da suka wuce ne gwamnatin jihar Anambra, a karkashin jagorancin sabon gwamna Farfesa Charles Soludo, ta umurci ma'aikata su kawo karshen zaman gida na kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, ta hanyar fara bayyana a wuraren aikinsu a kowace Litinin, ko kuma gwamnati ta dauki mataki akansu.
Kwamred Chinwe Orizu shugabar kungiyar kwadago ta jihar Anambra ta ce Farfesa Soludo sabon gwamna ne da ya fara aiki, kuma yana aikinsa ne bisa wannan umurnin da ya bada. Amma idan har zai iya tabbatar masu da tsaro, basu da matsala da zuwa aiki a ranar Litinin.
A nashi bayani, tsohon shugaban kungiyar ma'aikatan lafiya a jihar Kwamred Jerry Nnubia ya ce Idan gwamnati tana iya samar da isasshen tsaro, yana ganin jama'a zasu fita gudanar da harkokinsu ba tare da wani tsoro ba. Yanzu dai kowa na tsoro, ba wanda ke son sadaukar da ransa, duk da cewa ana tabka asara da wannan zaman gidan da ake yi a kowace Litinin.
To sai dai gwamnatin jihar Anambra tana mai cewa ta bada umurnin zuwa aikin ne saboda ba matsalar tsaro ba ce ke sa ma'aikata zaman gida a ranar Litinin a cewar sakataren gwamnatin jihar Farfesa Osita Chilobelu.
Ya ce ma'aikata da dama yanzu sun dauki ranar Litinin a matsayin ranar hutu. Bisa ga cewarsa, wamnati tana da motocin jigilar ma'aikata daga sassa daban-daban na jihar, amma basa amfani da wannan damar. Ya ce bai ga dalilin da ya sa wadanda suke da hanyar zuwa aiki basa zuwa ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Alphonsus Okoroigwe: