Kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da hakan wa muryar Amurka.
Ya ce, "Kwamishinan 'yan sanda CP Echeng Echeng da kansa ne ya jagoranci wani sashe na kwararrun ma'aikata suka fatattaki bata-garin, inda aka kashe daya daga cikinsu, sannan aka kwato bindiga guda da albarusai da kuma layoyi daga gurinsa."
Da ya ke bayyana abinda yasa 'yan bindiga ke ta kai hari ofisoshin 'yan sanda a jihar Anambra a 'yan kwanakin nan, Mista Chisom Igboko wani mai fashin baki kan lamuran yau da kullum ya ce, "Wadannan martanoni ne daga bata-gari. Kuma wannan yana nuni da cewa matakan da gwamnati take dauka na yin tasiri akansu, kuma suna bijirewa ne da wadannan hare-haren da suke kai wa, musamman bayan sabon gwamnan jihar Charles Soludo ya ayyana kawo karshen zaman gida da al'umma ke yi a kowace ranar Litinin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: