Jama’a na ci gaba da bayyana matsayin su bayan da sakamakon da aka tattara a zaben shugaban Amurka suka yi nuni da dan takarar jam’iyar Democrate Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba.
Jama’a na ci gaba da bayyana matsayinsu bayan da kafafen yada labaran Amurka suka yi hasashen dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ne ya lashe zaben Shugaban kasar Amurka duk da cewa dan takarar jam’iyyar Republican Shugaba Donald Trump bai amince da sakamakon ba.
Yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban Amurka, jama'a a nahiyar Afirka na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan yadda suke kallon wannan zabe mai cike da tarihi.
Yayin da hankalin kasashen duniya ya karkata kan zaben shugaban kasa na Amurka da za a yi ranar Talata 3 ga watan Nuwamba masu rajin kare dimokradiyya da masu bin diddigin siyasar duniya a Nijer na ci gaba da bayyana matsayinsu game da yadda suke kallon zaben.
‘Yan hamayyar a majalisar dokokin kasar sun yi wannan kiran ne saboda zargin MInistan cikin gidan da sakatarensa da nuna bangaranci a rikicin shugabancin da ake fama da shi a jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Firai Minista Hama Amadou, zargin da suka ce ba shi da tushe.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijer ya bukaci mutanen da suka sace wani Ba-Amurke a ranar Talata a garin Masallata dake yammacin birnin Konni, su gaggauta sakinsa.
A jamhuriyar Nijar, hukumar kula da shige da ficin kaya ta kafa wasu sabbin dokokin aikin fiton kaya da nufin magance matsalolin da ake fuskanta a tsakanin jami’an kwastam da ‘yan kasuwa da kuma masu aikin sufuri.
Gwamnatin Amurka ta tallafa wa iyallan sojojin da ambaliyar ruwa ta haddasa wa barna a jamhuriyar Nijer da wasu kayakin rigakafin cutar kwalara da na zazzabin cizon sauro wadanda darajarsu ta haura miliyon 20 na cfa.
Yayin da alkaluma ke nuna cewa cutar maleriya ta yi tsanani a Jamhuriyar Nijar a wannan shekarar, alamu na nuna cewa mutane wajen 2000 ne cutar ta hallaka a kasar bana.
A safiyar ranar Litinin 12 ga watan Oktoba ne aka yi bukin bayar da tallafin kudaden kungiyar Tarayyar Turai ga wasu kungiyoyin cikin gida a Nijar masu ayyukan kyautata rayuwar al’uma.
A Jamhuriyar Nijer kimanin watanni 2 bayan da ambaliyar ruwa ta tilasta wasu mazaunan birnin Yamai samun mafaka a makarantun boko sanadiyar rugujewar gidajensu gwammnatin kasar ta fara kwashe wadanan mutane don mayar da su wani sansani na musamman.
A jamhuriyar Nijer, dan takarar jam’iyar RANAA, Dr Hamidou Mamadou Abdou ya sha alwashin hukunta mahandama dukiyar jama’a idan ya ci zaben Shugaban kasa.
A yayin da aka cika shekaru 3 da rasuwar wasu sojojin Amurka 4 da na Nijar 4 sakamakon kwanton baunar da ya rutsa da su a ranar 4 ga watan okotoban shekarar 2017 a kauyen Tongo Tongo, Ofishin jakadancin Amurka a birnin Yamai ya shirya wani taron addu’o'i a domin tunawa da su.
Yau biyar ga watan Oktoba kasashen duniya ke bikin tunawa da ranar malaman makaranta wace Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin karrama malamai saboda gudunmuwar da suke bayarwa wajen ilmantar da al’umomin duniya.
Wata sabuwa kuma ta kunno kai game da takarar sanannen dan adawar Jamhuriyar Nijer dinnan, Hama Amadou. Wannan karon takaddama ake yi kan rashin rajistarsa.
A jamhuriyar Nijar ‘yan takarar zaben shugaban kasa na ci gaba da kunno kai a yayin da ya rage watanni 3 kacal ayi zaben kasar.
Ganin yadda kafafen sada zumunta ke matukar tasiri a lokacin zabe, hukumar zaben Janhuriyar Nijar da sauran masu ruwa da tsaki sun tashi haikan wajen ankarar da matasa muhimmancin amfani da kafafen yadda ya kamata.
A jamhuriyar Nijer madugun ‘yan hamayya, Hama Amadou na jam’iyar Moden Lumana ya yi ikirarin cewa ba za a iya hana masa shiga zaben da kasar ke shirin gudanarwa a watan disamban dake tafe ba
Ta leko ta koma ga batun sake bude makarantu a Janhuriyar Nijer ganin yadda ambaliyar ta hana, bayan dan sassaucin da ake ganin an dan samu game da annobar cutar corona, wadda ta sa aka dage tun farko.
A jamhuriyar Nijar, a yayin wani taro da ta gudanar a karshen mako a garin Dosso, jam’iyyar Moden Lumana ta jaddada madugun ‘yan adawa Hama Amadou a matsayin dan takararta a zaben watan Disamba mai zuwa da nufin kalubalantar jam'iyyar PNDS Tarayya wacce suke zargi da jefa kasar cikin matsaloli.
Domin Kari