Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Ranar Bude Makarantu a Nijer Saboda Ambaliyar Ruwa


Ambaliyar Ruwa A Niger
Ambaliyar Ruwa A Niger

Ta leko ta koma ga batun sake bude makarantu a Janhuriyar Nijer ganin yadda ambaliyar ta hana, bayan dan sassaucin da ake ganin an dan samu game da annobar cutar corona, wadda ta sa aka dage tun farko.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta bada sanarwar daga ranar sake bude makarantu daga 1 ga watan Oktoba zuwa 15 ga wata, da nufin samun isasshen lokacin gyaran wuraren da za a yi amfani da su don tsugunar da mutanen da ambaliyar ruwa ta ruguza gidajensu.

Kawo yanzu an kiyasta cewa gidaje 32,959 ne suka ruguje sanadiyyar ambaliyar ruwa a fadin kasar, lamarin da ya shafi mutane sama da 350,915 wadanda galibinsu suka nemi mafaka a makaratu daban daban, dalili kenan da hukumomi kasar suka yanke shawarar daga ranar komawa makarantu, a cewar kakakin gwamnatin Nijer, Minista Abdourahamane Zakaria yayin da yake shaida wa wakilin muryar Amurka ta wayar tarho.

Baya ga asarar gidaje da dukiyoyi, ruwan saman da ake tafkawa kamar da bakin kwarya a fadin kasar ya hallaka mutane sama da 70 tare da haddasa lalacewar dubban gonaki da mutuwar dimbin dabobi, lamarin da ya sa gwamnatin kasar bude wata gidauniya da nufin tattara dubban miliyoyin cfa don tallafawa al’ummar kasar da bala’in ya rutsa da su.

Saurari cikakken bayanin Souley Barma cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG