Sabon ce-ce-ku-ce ya barke a Jamhuriyar Nijer, bayan da aka gano cewa dan takarar jam’iyar hamayyya ta Moden Lumana, wato tsohon Fra Minista Hama Amadou, bai yi rajistar zabe ba. A yayin da magoya bayan jam’iyar PNDS mai mulki ke kallon abin tamkar wani shingen da zai hana wa jagoran na ‘yan adawa shiga zaben na watan Disamban 2020, su kuma magoya bayansa cewa su ke takarar zakaransu ta na nan daram.
Wannan sabuwar dambarwa ta taso ne bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa, binciken takardun rajistar da ke hannun hukumar zabe ya gano tsohon Fra Minista Hama Amadou bai yi rajistar zabe ba, abinda ake ganin zai shafi sahihancin takararsa a gaban kotun tsarin mulkin kasa.
Wani na hannun damansa, Bana Ibrahim, ya ce, yana da ja akan wannan hasashe.
Kakakin jam’iyar PNDS mai mulkin kasa, Assoumana Mahamadou, ya ce, yana kalon abin tamkar wani matakin samun nasara a zaben dake tafe.
Masanin doka, Dr. Boubacar Amadou Hassan ya alakanta rashin rajistar Hama Amadou da hukuncin da aka yi masa na daurin shekara daya a kurkuku bayan da aka same shi da hannun a wata badakalar sayan jarirai.
Saurari cikakken rahoton Souley Barma ta sauti:
Facebook Forum