Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Tunawa Da Sojojin Amurka Da Nijar Da Suka Mutu a Yankin Tillaberi


Taron Tunawa da Sojojin Amurka da Nijar
Taron Tunawa da Sojojin Amurka da Nijar

A yayin da aka cika shekaru 3 da rasuwar wasu sojojin Amurka 4 da na Nijar 4 sakamakon kwanton baunar da ya rutsa da su a ranar 4 ga watan okotoban shekarar 2017 a kauyen Tongo Tongo, Ofishin jakadancin Amurka a birnin Yamai ya shirya wani taron addu’o'i a domin tunawa da su. 

A lokacin da ake bikin tunawa da sojojin Amurka da Nijar da suka kwanta dama a ofshin jakadancin Amurka da ke birnin Yamai, Leftanal Abdoulkader Ali, na rundunar mayakan Nijar ya zayyano sunayen sojojin 8 da suka mutu bayan wani fada da aka yi a kauyen Tango Tango da ke yankin Tillaberi, inda ‘yan ta’adda suka yi musu kwantan bauna.

Ali ya kara da cewa jarumtakar da wadannan sojojin na Amurka 4 da takwarorin aikinsu 4 na Nijar suka nuna a yayin wannan gumurzu na ranar 4 ga watan Oktoba a shekarar 2017 ya sa gwamanatin Amurka ware wani sashe na musamman domin karramasu.

Jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijar, Ambasada Eric Whitaker ya ce “Wadanan mazaje ‘yan Nijar da Amurkawa gwarzaye ne. Muna jinjina masu kuma ba za mu taba mantawa da sadaukar da kan da suka yi ba. Muna fatan Allah ya jikansu.”

Ya kara da cewa, a yayin da a yau muke karrama wadanan askarawan da suka rasu a fagen daga ya zama wajibi a daya gefe mu isar da godiya da yabo ga sojojin Amurka, da Nijar, da na Faransa saboda daukin da suka kai a daidai lokacin da fadan ya yi tsanani.

Zaman addu’oin na wannan rana ya kasance wani lokacin bayar da lambar yabo ga sojijn wadannan kasashe 2 saboda yadda suka hada kansu domin tunkarar maharan na kauyen Tongo Tongo.

Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Nijar, Alhaji Idi Bara’u, ya ce gwamnatin Amurka ta karrama sojojin da manyan lambobin yabo da ake ba sojojin Amurka, saboda sojojin sun rasa ransu ne a kokarin taimakawa wajen samar da tsaro a Nijar.

Za dai a kafa duwatsu 8 dauke da sunayen kowanne daga cikin wadanan sojoji a wani sashe na musamman da aka kebe a sabon ofishin jakadancin Amurka a Nijar da nufin girmamawa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG