Kakakin ofishin jakadancin Amurka a Nijer Stephen Dreikorn, ya tabbatar da rahotan sace wani dan kasar Amurka a garin Masallata dake yammacin birnin konni a jihar Tahoua, wanda ‘yan bindiga ke ci gaba da garkuwa da shi.
Yanzu haka jami’an kasashen biyu sun hada kai don ganin an ceto wannan mutumin da aka sacen daga hannun mutanen da suka yi garkuwa da shi.
Gudunmawar jama’a wajen bayar da bayanai itace hanyar da ofishin jakadancin Amurka ke ganin za ta iya taimakawa a gano inda aka boye wannan Ba-Amurken.
Rahotanni sun baiyana cewa a cikin daren Litinin, wayewar ranar Talata ne, wasu mutane dauke da bindigogi suka kai sumame a garkar da wasu Amurkawa ke zaune kusa da garin Masallata, dake yammacin birnin konni inda suka yi awon gaba da daya daga cikinsu mai suna Philipe Walton, mai shekaru 27 a duniya.
Duk da yake ya zuwa yanzu ba wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan al’amari, wasu na alakanta abin da aiyukan masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum