Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Sahrhin Siyasa A Nijer Sun Ce Trump Ya Rungumi Kaddara


Trump
Trump

Jama’a na ci gaba da bayyana matsayin su bayan da sakamakon da aka tattara a zaben shugaban Amurka suka yi nuni da dan takarar jam’iyar Democrate Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Sai dai dan takarar jam’iyar Republican shugaban kasa Donald Trump, ya kudiri aniyar kalubalantar wannan sakamako a kotu.

Sakamakon wanda ya bayyana a yammacin ranar Asabar yayi nuni da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden najam’iyar Democrat mai kuri’un wakillai 273 ya doki abokin karawarsa wato shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyar Republican mai kuri’u 214 abin da wani dan rajin kare dimokradiya Abdou Elhadji Idi ya ce bai zo da mamaki ba.

Tuni dai Donald Trump da magoya bayansa suka yi watsi da wannan sakamako saboda zargin tafka magudi lamarin da yasa suka yanke shawarar garzayawa kotu matakin da wani mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Alkassoum Abdourahaman ya ce ya yi daidai.

Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou kamar sauran takwarorinsa na duniya, ya taya Joe Biden murnar samun wannan nasara tare da fatan dorewar dadaddiyar huldar Amurka da Nijer, sai dai lura da kullin da ke tattare da wannan zabe yasa masana ke ganin abin na bukatar taka tsantsan.

A ra’ayin Abdou Elhadji Idi bakin alkalami ya riga ya bushe saboda haka dole Donald Trump da mutanensa su rungumi kaddara.

Yanzu kam hankali ya karkata wajen kasar ta Amurka domin jin yadda za ta kaya game da wannan sabuwar dambarwa mai kamanni sak da irin wadanda aka saba gani a wasu kasashen Afrika.

Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana Karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG