Wannan shine karon farko da Dr Hamidou Mamadou Abdou ke kiran taron manema labarai tun bayan da jam’iyar RANAA ta bayyana shi a matsayin wanda zai wakilce ta a zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan disamba, koda yake ya yi amannar cewa akwai alamun kura kurai tattare da ayyukan tsare tsaren zabukan dake tafe, Dr Hamidou ya ce batun shiga wannan fafatawa ba fashi.
To amma a cewarsa har yanzu akwai hanyoyin warware matsalolin da suka janyo korafe korafe daga bangaren ‘yan hamayya.
Yaki da mahandama dukiyar jama’a da yaki da talauci sune mahimman abubuwan da dan takarar jam’iyar RANAA ya sha alwashin maida hankali akansu don ganin talakan Nijer ya fara morar arzikin kasa, inji shi.
A ranar 28 ga watan Disamban 2019 ne taron congres na sabuwar jam’iyyar RANAA ya zabi shugabanta Dr Hamidou Mamadou Abdou a matsayin dan takarar zaben shugaban kasa.
Dr Hamidou, wanda dan Nijer ne mai zama a kasar Canada, ya kafa kamfanin kasa da kasa na kashin kansa dake gudanar da ayyuka a fannoni da dama a kasahen Afrika, a cewarsa damuwa a game da wahalhalun da talakawa ke fama da su ya sa shi yanke shawarar shiga siyasa.
Facebook Forum