Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hama Amodou Ya Ce Ba Za a Iya Hana Shi Shiga Zaben Nijer Ba


A jamhuriyar Nijer madugun ‘yan hamayya, Hama Amadou na jam’iyar Moden Lumana ya yi ikirarin cewa ba za a iya hana masa shiga zaben da kasar ke shirin gudanarwa a watan disamban dake tafe ba

A taron manema labaran da ya kira a washe garin taron da ya bayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyar Moden Lumana a zaben shugaban kasa na ranar 27 ga watan disambar 2020, tsohon Fra Minista Hama Amadou ya jaddada cewa batun shiga wannan zabe ba fashi..

Yace kundin tsarin mulki a sashensa na 47 ya bayyana a fili karara cewa sharuda 2 ne aka gindaya wa masu neman shugabancin kasa. Da farko ya zama dole mutun ya kasance dan Nijer na asali. A cewarsa Wannan sharadi ya cika shi sannan ya kara da cewa dokar kasa ta bayyana cewa dan Nijer na asali shine wanda iyayensa ‘yan kasa ne da aka haifa a Nijer.

Sharadi na 2 shine mutun ya na da ‘yancin shi na dan kasa da na siyasa shi ma wannan ‘yanci yana da su a cewarsa. Watakila za a ce kotu ta yanke min hukuncin zaman wakafin shekara 1 to amma wannan wani abu ne da abokan gabar siyasa suka kitsa da nufin kawar da ni daga fagen siyasa saboda haka suka bukaci alkalin Procureur ya dauki irin wannan mataki a kaina amma kuma sauran alkalan da ke alhakin yanke hukunci suka yi watsi da wannan bukata.

Tuni dai furicin na tsohon Fra Mnista ya janyo martani daga jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki. Siraji Issaka na daga cikin jiga jiganta.

Hama Amadou ya yi ikirarin cewa akwai yiyuwar abubuwan da suka faru a kasar Mali su wakana a Nijer muddin aka hana masa shiga zaben dake tafe.

Yace ya kamata a dawo kan turbar dimokradiyya a dawo kan hanyar haske a koma kan hanyar shugabanci domin jama’ar kasa ba wai maganar bangarenci ko wani gungu ba. Aiki ne da ya rataya a wuyar al’umma saboda haka wadanda ke tunanin ina kira ne ga sojoji to su cire wannan tunani daga kawunansu domin a cewarsa shi dan siyasa ne kuma farar hula sabili kenan komai nasa ya ta'allaka ne akan ayyukan fararen hula.

To sai dai jam’iyyar ta PNDS na kallon wannan a matsayin wani turji inji Siraji Issaka.

Saurara cikakken rahoton Souley Barma a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG