Sakamakon zaben wanda ya bayyana a yammacin ranar Asabar 7 ga watan Nuwamba ya yi nuni da cewa tsohon mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden na jam’iyyar Democrat da ya samu kuri’un wakillai 279 ne ya doke abokin karawarsa wato Shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyyar Republican wanda ya samu kuri’u 214, abinda wani dan rajin kare dimokradiya Abdou Elhadji Idi ya ce bai zo da mamaki ba.
Tuni dai Donald Trump da magoya bayansa suka yi watsi da wannan sakamako saboda zargin an tafka magudi lamarin da ya sa suka yanke shawarar garzayawa kotu, matakin da wani mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum Alkassoum Abdourahaman ya ce ya yi daidai.
Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou kamar sauran takwarorinsa na duniya ya taya Joe Biden murnar samun wannan nasara tare da fatan dorewar dadaddiyar huldar Amurka da Nijer, to sai dai lura da kullin da ke tattare da wannan zabe ya sa masana ke ganin abin na bukatar taka-tsantsan.
A ra’ayin Abdou Elhadji Idi, bakin alkalami ya riga ya bushe saboda haka dole Donald Trump da mutanensa su rungumi kaddara.
Yanzu dai hankali ya karkata kan Amurka domin jin yadda za ta kaya game da wannan sabuwar dambarwa mai kama da irin wadda aka saba gani a wasu kasashen Afrika.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum