Mafi akasarin jama’a a Jamhuriyar Nijar wadanda wannan zabe ya ja hankulansu na ci gaba tsokaci game da tsaikon da ke tattare da ayyukan kidayar kuri’un zaben Amurka na ranar 3 ga watan November.
Yayin da wasu ke ganin tamkar wata manakisa ce, wasu kuwa na cewa ci gaban dimokradiya ne mafarin hakan.
Sabanin yadda aka saba ji a yayin zabukan kasashen Afrika, galibin jama’ar nahiyar Afrika na yabawa da yadda zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba ya gudana a Amurka, saboda gamsuwa da tsarin da aka yi amfani da shi wajen bai wa ‘yan kasar damar kada kuri’arsu.
Rabiou Abba Dan Illela na daga cikin wadanda ke begen tsarin zaben kasar Amurka inda ya ke cewa "Sun gamsu da yadda zaben ya gudana, ganin yadda aka fara shi sama da makonnin biyu da suka wuce.
Sai dai a ta sa fahimtar wani matashin dan takarda Alio Maifada na cewa bai ga laifin komai ba idan dan takara ya kai kara a gaban kotu saboda zargin magudi.
A bangare daya kuwa, wasu na ganin cewar wannan gazawa ce, ganin yadda tun kamun a sanar da sakamkon, daya daga cikin 'yan takarar na ikirarin cewar shi ya lashe zaben.
Hakan babban kalubale ne ga dimokradiyya, musamman idan aka duba kasar Amurka ce aka samu wanna matsalar
Halin rashin tabbas din da ake ciki a kokarin tantance wanda ya yi nasara kwanaki akalla hudu bayan wannan zabe wani abu ne da ke saka fafatawar ta 3 ga watan Nuwamba a jerin zabukan da suka fi daukar hankalin jama’a a tarihin duniya.
Ga karin bayanai a rahoton Souley Moumouni Barma a cikin sauti.
Facebook Forum