Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Hamayya a Nijer Sun Bukaci Shugaban Kasa Ya Kori Ministan Cikin Gida Da Sakatarensa


Ginin majalisar dokokin kasa a Yamai, babban birnin Nijar.
Ginin majalisar dokokin kasa a Yamai, babban birnin Nijar.

‘Yan hamayyar a majalisar dokokin kasar sun yi wannan kiran ne saboda zargin MInistan cikin gidan da sakatarensa da nuna bangaranci a rikicin shugabancin da ake fama da shi a jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Firai Minista Hama Amadou, zargin da suka ce ba shi da tushe.

Wasikar da magatakardan ofishin ministan cikin gida ya aika wa Oumarou Noma a matsayin halattaccen shugaban jam’iyyar Moden Lumana a wani lokacin da wata kotun birnin Yamai ta haramta masa amfani da sunan wannan jam’iyya ya sa ‘yan hamayya a majalisar dokoki jan hankalin shugaban kasa Issouhou Mahamadou game da abinda suka ce barazana ce ga dimokradiya kamar yadda suka bayyana a wata sanarwar da suka fitar.

Honarabul Maman Djibo, dan majalisa ne daga jam’iyar RDR Canji, ya ce sun yi kira ne don jan hankalin shugaba Issouhou Mahamadoou a matsayin shi na shugaban alkalai na kasa akan me ya sa alkalan za su tsaida shari’a har sau uku, don haka ya kamata shugaban ya kare mutuncin shi da na alkalan dangane da zartar da shira’ar don a ga gaskiya ta tabbata. ‘Yan hamayyar sun ci gaba da cewa daukar matakan hukunta wadanan jami’ai ya zama wajibi.

To sai dai a wata sanarwar da ma’aikatar cikin gidan ta bayar a gidan rediyon gwamnatin Nijer, Minista Alkache Alhada da sakatarensa Ider Adamou, sun bayyana cewa ba su kauce wa doka ba wajen amincewa da halaccin taron da bangaren Oumarou Noma ya shirya a watan Satumban da ya shige a Dosso. Suna masu cewa dukkan masu ja da wannan mataki suna da hanyar kalubalantar abin a gaban kotu..

A watan da ya shige dayan bangaren Moden lumana ya bayyana madugun ‘yan hamayya Hama Amadou a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben 27 ga watan Disamaba na shekarar 2020, dalili kenan mukarrabansa ke kallon matakin bai wa Oumarou Noma hurumin shugabancin jam’iyyar tamkar wata makarkashiya ce da aka kitsa dagangan da nufin hanawa tsohon Firai Ministan shiga wannan zabe. Zargin da jam’iyyar PNDS mai mulki ke cewa babu kamshin gaskiya a tare da shi.

Saurari cikakken rahoton Sule Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG