Gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso ta bayyana takaici a game da abinda ta kira halin ko in kular da wasu kasashe abokan kawancenta ke nuna mata dangane da halin tabarbarewar sha’anin tsaron da ta tsinci kanta ciki sakamakon aika - aikar ‘yan ta’adda yau shekaru a kalla 7.
Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun kama wasu fitattun mawakan Najeriya lokacin da su ke kokarin hada takardu don samun fasfon kasar ta Nijer da nufin zuwa kasashen turai.
A wata hira da shugaban kungiyar makafi ya kwatanta girman wannan matsala da kuma hanyoyin da yake ganin idan aka bi su za a warware wannan kulli.
Shuwagabanin hukumomin yaki da cin hanci daga kasashen Afrika ta yamma suna gudanar da taron wuni 1 a birnin Yamai a karkashin inuwar kungiyarsu ta NACIWA ko RINLCAO.
Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar ta yi bitar ayyukan rijistar da ta gudanar a watan Oktoban da ya gabata a wasu kasashen waje a ci gaba da shirye-shiryen zaben mutanen da za su wakilci ‘yan kasar ta Nijar mazauna ketare a majalissar dokoki.
Binciken da kungiyar ROTAB Niger ta ce ta gudanar a daukacin yankunan da ke da arzikin ma’adanai ya bada damar gano rashin adalcin da ake yi wa mata da yara a Nijar.
A cikin shirin na wannan makon mun duba halin da malaman ke ciki domin ba ya ga karancin kayan aiki, wadanan malamai na fatan ganin an bullo da hanyoyin ba su horo ta yadda za su sami kwarewar da ke daidai da ci gaban da zamani ya zo da shi don taimakawa daliban.
Taron hukumomi da kungiyoyin kasashen Afrika masu rajin kare hakkin dan Adam karo na 73 da ke gudana a kasar Gambia, ya yaba da yadda jamhuriyar Nijer ta maida hankali wajen mutunta wasu mahimman ‘yancin dan Adam.
Shugabannin hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH sun kai ziyara a asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka ji rauni a yayin ruwan wutar da jiragen sojan saman Nijar suka yi.
An kafa makarantar ne a wani bangare na matakan shigar da nakasassu a sha’anin ilimin boko ta yadda za su tashi da tunanin rungumar kwakkwarar madogarar rayuwa a maimakon shiga harakar bara.
Hukumomin Nijer sun fara nazarin sabbin hanyoyin magance matsalar bara bayan la’akari da yadda wasu ‘yan kasar dauke da yara kanana ke kwarara zuwa kasashen waje da nufin rungumar wannan kaskantacciyar sana'a duk da jan hankalin da hukumomi da kungiyoyi ke yi.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer da Kungiyar Tarayyar Turai sun saka hannu akan wata yarjejeniya wace a karkashinta kungiyar EU ta amince ta ba kasar ta Nijer tallafin biliyan kusan 10 na kudaden cfa wadanda za a yi amfani da su don bunkasa sha’anin ilimi.
Fitaccen dan siyasa a Jamhuriyar Nijar Doudou Rahama na hannun daman tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman da magoya bayansa ,sun bada sanarwar canza sheka daga jam’iyar RDR Canji zuwa PNDS Tarayya ta shugaba Mohamed Bazoum.
Ma’aikatar tsaron Nijer ta sanar cewa wasu jiragen sojan kasar sun hallaka ‘yan ta’adda a wata mahakar zinare da ke kauyen Tamou na gundumar Say a jihar Tilabery, sai dai wasu ‘yan rajin kare hakkin bil'adama na ganin akwai bukatar a gudanar da bincike don gano zahirin abinda ya faru.
Magoya bayan jam’iyar Moden Lumana ta tsohon Firai Minista Hama Amadou sun gudanar da babban taro domin bitar halin da jam’iyar ke ciki.
Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale ya jaddada aniyar ci gaba da gwagwarmayar kare muradun kasashen Afirka bayan da ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai ya bada sanarwar soke takardar bizar da ke bashi izinin shiga kasar ta Faransa.
Wasu kungiyoyin fafutika na hadakar M62 a Jamhuriyar Nijer sun kudiri aniyar gudanar da zanga zangar lumana a ranar 30 ga watan nan na Oktoba da nufin tada hukumomi daga barci dangane da wasu tarin matsalolin da suka addabi jama’a.
A Nijer, hadakar kungiyoyin fafutikar M62 sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 30 ga watan Oktoba don tada hukumomi daga barci a kan matsalolin da suka addabi jama’a ciki har da sha’anin tsaro, lamarin da ke nuna rashin tasirin girke rundunar sojojin Faransa a kasar.
Wata ‘yar majalissar dokokin kasa daga bangaren masu rinjaye a Jamhuriyar Nijar, ta shawarci takwarorinta ‘yan majalissa da ma hukumomi akan bukatar nazarin hanyoyin warware sarkakiyar dake tattare da dokokin kasar game da batun mu’amular mutane masu jinsi daya.
Jam’iyar hamayya ta ADR Mahita a Jamhuiriyar Nijar ta bayyana damuwa dangane da abinda ta kira halin kuncin rayuwar da jama’ar kasar ke ciki sanadiyar wasu tarin matsaloli da suka hada da lalacewar lamuran tsaro da durkushewar tattalin arziki, ilimi da kiwon lafiya.
Domin Kari