A karshen makon jiya ne wadanan mawaka suka fada hannun jami’an shigi da fici a birnin Yamai kafin wani alkali ya tura su kurkuku har zuwa lokacin da za a kammala bincike akan wannan batu da ke farfado da mahawara a game da batun yawaitar takardun boge.
Wadanan mawaka da suka hada da Mubarak Abdulkarim da aka fi sani da 442 da wani abokinsa Ola sun zo birnin Yamai ne takanas domin neman fasfo a cibiyar ma’aikatar shigi da fici Direction de la Surveillance du territoire wato DST a takaice.
Bincike a kan takardun da suka gabatar a ofishin kula da fasfo ya bada damar gano cewa takardun boge ne wadanan ‘yan Najeriya dake samun rakiyar wani abokinsu dan Nijer suka zo da su, mafari aka cafke su inda suka yi kwanaki 3 a hannun ‘yan sanda kafin daga bisani a wuce da su gidan yari.
Tuni dai wannan labari ya karade kafafen sada zumunta inda wasu ke cewa an bukaci wadanan mawaka su biya miliyoyin cfa a matsayin kudaden beli to sai dai Shugaban kungiyar ‘yan wasan Hausa Ibrahim Yusuf da aka fi sani da Mitou Baban Pele wanda ya ziyarci wadanan mawaka a gidan yarin da suke tsare ya karyata batun biyan kudi.
Shugaban kungiyar Jangorzo ta masu kamfanonin finanai da mawakan Hausa Makodin Gobir Nohou Dan Maradi na cewa, rashin neman shawara ne dalilan abinda ya faru da wadanan takwarorinsu ‘yan Najeriya.
A cewar alkali mai tuhuma Procureur de la Republique akwai yiyuwar binciken wadanan mawaka 442 da Ola ya kwashe watanni 6 wanda kuma idan ba a gano haske ba doka ta bada dama a sake sabinta wa’adin bincike na tsawon watanni 6 kafin a yanke hukunci.
Saurari rahoton cikin sauti :