Hakan na zuwa ne biyo bayan shafe lokaci mai tsawo da aka yi ba tare da jin duriyarta ba a fagen siyasar kasar sakamakon cafke wasu jiga jiganta a washegarin babban zaben da aka bayyana shugaba Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara.
Wakilai sama da 300 ne daga jihohi 8 na Nijar suka hallara a wannan taro dake matsayin na farfado da ayyukan jam’iyar Moden Lumana madugar jam’iyun hamayya wace ta tsinci kanta cikin halin tsaka wuya a washegarin zaben 2020 inda har wasu kusoshi suka yi yunkurin kwace ragamarta daga hannun tsohon Firai Minista Hama Amadou da ya kafa ta.
Yanzu haka wasu manyan jiga- jigan jam’iyar da aka kama a yayin tarzomar watsi da sakamakon zaben da ya gabata na can kulle a kurkuku saboda zarginsu da yunkurin tada zaune tsaye.
Cikinsu har da Hama Amadou da ya fice daga gidan yari zuwa kasar waje da nufin ganin likita, lamarin da ake ganin shi ma ya gurgunta ayyukan jam’iyar kamar yadda canza shekar wasu shugabaninta ta haddasa babban koma baya.
A hirar shi da Muryar Amurka, Bana Ibrahim daya daga cikin shugabanin matasa Moden Lumana, ya ce sun fuskanci matsaloli da yawa biyo bayan kama wasu 'yan jam'iyyun su da aka yi saboda haka bai basu dama su gudanar da aikinsu kamar yadda su ke so don yunkurin da su ka sa a gaba na ganin a sako 'yan jam'iyansu da aka kama.
Wannan ya sa taron na uwar jam’iya ya dauki lokaci mai tsawo yana tantauna makomarsu yayinda ake sauraran soma zaman shara’arsu a wannan mako.
Jam’iyar Lumana wace kotu ta yi watsi da takardun dan takararta Hama Amadou a zaben 2020, ta umurci magoya bayanta su kada wa dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman kuri'a tun a zagayen farko, lamarin da ya bashi damar kaiwa zagaye na 2 inda dan takarar PNDS Tarayya Mohamed Bazoum ya doke shi.
Cikakkiyar dasawar dake tsakanin hukumomi na yau da wasu manyan shugabanin jam’iyar ta ‘yan hamayya ta sa wasu ‘ya'yanta soma zarginsu da zama ‘yan amshin shatan gwamnati.
Saurari rahoton cikin sauti: