NIAMEY, NIGER - A cikin shirin na wannan makon mun nufi Damagaram a Jamhuriyar Nijar don duba halin da ake ciki a makarantar firamari ta makafi da ake kira birnin Garçon wacce aka kafa a shekarar 2000.
Shekaru sama da 20 bayan bude wannan makaranta ana iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu domin dimbin ma’aikata makafi da ake damawa da su a yau a fannoni daban-daban sun bi ta wannan makaranta.
Sai dai kuma bayanai na nunin a yau al’amuran karatu ba sa tafiya kamar yadda ya dace sakamakon tarin matsalolin da ake fuskanta kamar yadda Darektan makarantar ta birnin Garçon Ibrahim Moustapha Titi ya bayyana a hirarsu da Muryar Amurka.
Saurari cikakken shirin daga Souley Moumouni Barma: