Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fafutika Sun Kudiri Aniyar Yin Zanga-Zangar Tada Hukumomin Nijer Daga Barci Kan Matsalolin Jama'a


Zanga Zanga
Zanga Zanga

A Nijer, hadakar kungiyoyin fafutikar M62 sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 30 ga watan Oktoba don tada hukumomi daga barci a kan matsalolin da suka addabi jama’a ciki har da sha’anin tsaro, lamarin da ke nuna rashin tasirin girke rundunar sojojin Faransa a kasar.

Tsadar farashin kayan abinci da sauran ababen masarufi na daga cikin matsalolin da hadakar M62 ta ce hukumomin Nijer sun yi buris dasu a wani lokaci da ake fama da karancin kudi a hannun jama’a, yayin da a wasu yankunan aika-aikar ‘yan bindiga ta hana talakawa gudanar da ayyuka a gonaki, hasali ma dubban mutane sun kauracewa garuruwansu sanadiyyar tashe-tashen hankulan. Wannan ya sa kungiyoyin suka kudiri aniyar fitowa kan titunan birnin Yamai a ranar Lahadi 30 ga watan Oktoban 2022 domin ankarar da mahukunta halin da ake ciki kamar yadda suka sanar a wani taron manema labarai.

Ibrahim Namaiwa mai magana da yawun wadannan kungiyoyi, ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakan yaki da tsadar rayuwa da ta yi wa jama’a katutu.

Matakin girke dakarun Barkhane a Nijer bayan ficewar rundunar daga kasar Mali wani abu ne da bai dace ‘yan kasa su aminta da shi ba a cewar M62, shi ya sa kungiyar ta bukaci jama’a su hallara a wannan zanga-zanga domin nuna bukatar ficewar sojan Faransa daga Nijer duk da cewa gwamnatin kasar ce ta nuna bukatar samun dauki daga kasashe aminanta.

Malan Gamatche Mahamadou, na daga cikin shika-shikan wannan hadaka, ya ce idan za a yi hulda da wata kasa to a yi ta bisa adalci da gaskiya ta yadda duk bangarori zasu amfana, a ganinsa dakarun Faransa da ke kasar basu da wani amfani.

Sai dai alamu na nunin an samu baraka a tsakanin jagororin wannan tafiya kamar yadda Falmata Taya mai magana da yawun bangaren Abdoulaye Saidou ta bayyana. Ta ce ya kamata kowa ya san ‘yan hadakar M62, saboda wasu ‘yan siyasa na amfani da wasu ‘yan kungiyar don bata musu rawa da kura.

To sai dai Ibrahim Namaiwa da ke kare bangaren Gamatche Mahamadou na cewa ba haka zancen ya ke ba.

A jajibirin ranar bukin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kan Nijer daga turawan mulkin mallaka ne hadakar M62 ta bada sanarwar shigowarta fagen gwagwarmaya, abinda ya bata damar shirya zanga-zangar lumana a ranar 18 ga watan Satumban 2022 a biranen Yamai da Dosso domin kalubalantar mahukunta akan matsalolin da ke da nasaba da sha’anin gudanar da mulkin kasa.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
XS
SM
MD
LG