Hukumar ta CENI ta ce ta gano cewa yawan mutanen da suka yi rijistar a wannan karon ya linka na shekarar 2015 saboda haka nan da ‘yan kwanakin da ke tafe za ta yi ayyukan tacewa kafin wallafa sunayen mutanen da suka cancanci samun katin zabe.
Shugaban hukumar zaben Nijer Me Issaka Sounna ya yi wa manema labarai bayani bitar ayyukan rajistar da hukumar ta gudanar daga ranar 15 zuwa 30 ga watan okotban 2022 a kasashe 15 wadanda suka hada da Aljeriya da Benin da Burkina Faso da Cameroun da Cote d’ivoire da Ghana da Mali da Najeriya da Morocco Senegal da Cadi da Togo da Belgiium da Faransa da Amurka.
Sounna ya ce an yi komai ba tare da wata matsala ba a yayin gudanar da wannan aiki na shirye-shiryen zaben mutanen da za su wakilici ‘yan nijar mazauna kasasen waje a majalissar dokokin kasa.
Mutane sama da 200,000 ne suka yi rijista a tsawon wadanan makwanni, abin da ke nuna alamun yadda ‘yan Nijar mazauna ketare ke daukan wannan zabe da muhimmanci.
Tun a watan Disambar 2020 ne ya kamata ‘yan Nijar mazauna ketare su halarci runfunan zabe wato lokaci guda da ‘yan kasar na cikin gida domin kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa.
Sai dai hakan ba ta samu ba sakamakon annobar coronar da ake fama da ita a wancan lokaci to amma ganin yadda kura ta lafa a mafi yawancin kasashen duniya ya sa hukumar CENI ta fara yunkurin shirya zaben da zai ba su damar turo mutane 5 da za su wakilce su a majalissar dokoki kamar yadda dokokin kasar Nijar suka yi tanadi.
Saurari rahoton a sauti: