Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Bitar 'Yancin Dan Adam A Nahiyar Afrika Ya Yaba Kokarin Hukumomin Nijer


Taron Bitar 'Yancin Dan Adam A Nahiyar Afrika Ya Yaba Wa Kokarin Hukumomin Nijer
Taron Bitar 'Yancin Dan Adam A Nahiyar Afrika Ya Yaba Wa Kokarin Hukumomin Nijer

Taron hukumomi da kungiyoyin kasashen Afrika masu rajin kare hakkin dan Adam karo na 73 da ke gudana a kasar Gambia, ya yaba da yadda  jamhuriyar Nijer ta maida hankali wajen mutunta wasu mahimman ‘yancin dan Adam.

Wannan na zuwa ne biyo bayan sabanin yadda aka gano kasashe da dama na nahiyar Afrika da gaza cika alkawulan dake kunshe a yarjejeniyar da suka sakawa hannu a wannan fanni.

Hukumomin shara’ar ta Nijer sun yi amfani da wannan dama don jaddada wa jama’a cewa ba za su taba amincewa da ‘yancin masu luwadi da ‘yan madigo ba a kasar.

A taron bitar da suka kira a gaban manema labarai a washegarin dawowarsu daga birnin Banjul, shugabanin tawagar Nijer a wannan taro sun ce sun zo da babban albishir mai nasaba da ‘yancin dan adam kasancewar ‘yancin dan adam na daga cikin sharudan da ya zama dole kasashe su cika kafin samun karbuwa a wajen sauran takwarorinsu na duniya.

Sakin ragamar ‘yancin fadin albarkacin baki a ‘yan shekarun nan 2 a Nijer wani mataki ne da ya yi matukar tasiri wajen canza kimar kasar a idon duniya .

Sai dai duk da yabon da suke sha, hukumomi sun ce Nijer ba za ta taba amincewa da ‘yancin ‘yan madigo da ‘yan luwadi ba, ballantana maganar auren jinsi.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

XS
SM
MD
LG