Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta jaddada aniyar soma zartar da tsarin inshorar manoma a shekarar 2023 da nufin takaita dimbin asarar da bala’in ambaliya da sauran illolin canjin yanayi ke haddasa wa manoma, makiyaya da masintan kasar a wannan lokaci da tallafin masu hannu da shuni ke karanci.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar rufe wasu makarantu masu zaman kansu dake horar da likitoci saboda zarginsu da rashin cika wasu mahimman ka’idodin da suka shafi sha’aniin kiwon lafiya.
Kungiyar kare hakkin jama’a da bunkasa dmokradiya a Jamhuriyar Nijar ta shirya wata mahawara a bainar jama’a da ta hada bangarorin siyasar kasar domin tantauna halin da ake ciki .
Ministan kudin Nijer ya sanar cewa kasar ta fuskanci cikas wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2022, lamarin da ake alakantawa da matsalolin tsaro, illolin yakin Rasha a Ukraine. Lura da wannan ya sa gwamnatin ta Nijer maida hankali akan maganar tattara kudaden harajin cikin gida a kasafin badi.
Mun samu bakuncin wani makaho da ya shahara a wani fannin da ba kasafai ake samun masu lalurar indanu cikinta ba.
Wasu sabbin jami’an kwastom da suka kammala horo a makarantar hafsoshin soja ta EFOFAN a Jamhuriyar NIjar, sun yi zaman dirshe a yau a ma’aikatar kudi ta kasa da nufin nuna kosawarsu a game da abinda suka kira tsaikon da ake fuskanta wajen ba su damar soma aiki.
Shuwagabanin kungiyoyin ci gaban jihar Maradi sun bayyana damuwa dangane da lalacewar al’amuran tsaro a yankin da masu satar mutane da barayin shanu ke cin karensu ba babbaka.
A yayin da matatar man SORAZ ke shirin dakatar da aiki don yin gyare gyare, Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta bada sanarwar daukar matakan riga kafi da nufin kauce wa karancin iskar gas a tsawon wannan lokaci. A saboda haka ta gargadi masu sana'ar iskar gas su mutunta tsarin farashin da aka kayyade.
A cikin shirin na wannan makon, a makon jiya shirin ya tantauna da wasu shugabanin makafin Najeriya da Nijar dake ci rani a kasar Ghana a dalilin dangantakar da ke tsakaninsu da sarkin makafi. Kamar yadda aka ji a baya wadanan nakasassu sun bayyana wa shirin nakasa dalilansu na tarewa a Ghana.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun yi karin haske dangane da matakin dakatar da shigar da man fetur zuwa kasar Mali.
A jamhuriyar Nijer kungiyoyin da ke bin diddigin sha’anin ma’adinai sun fara jan hankula a game da bukatar kafa asusun ajiyar wani kaso na kudaden shigar ma’adanai ta yadda watarana ‘ya'ya da jikoki za su mori wannan arziki a maimakon a bar su da irin illolin da ayyukan hakar ma’adanai ke haddasawa.
Gwamnatin Amurka ta bai wa jamhuriyar Nijar tallafin wasu motoci 51 wadanda darajarsu ta haura million 13 na dolar Amurka domin tallafa ma jami’an tsaron kasar a yakin da suke kafsawa da kungiyoyin ta’addancin Yankin Sahel.
Kamfanonin aikin haji da umra a Jamhuriyar Nijer sun kai karar hukumar alhazan kasar a kotu da neman a mayar masu da kudaden wasu maniyata sama da 100 da ba su sami tafiya kasar Saudiya ba a yayin hajin bana duk kuwa da cewa sun cike sharudan da suka wajabta a wuyan maniyata.
A Jamhuriyar Nijar, jiya Alhamis, 15 ga watan Satumba, aka yi shagulgulan baje kolin al’adun al’ummar Tubawa bayan da a shekarar 2020 shugabanin wannan kabila dake zaune a kasashen Nijar, Libya, da Chadi suka yanke shawarar ware ranar.
Ambaliyar ruwan da ake fuskanta a sassan Nijer sanadiyar ruwan saman da ake yi ta haddasa asarar rayukan mutane fiye da 100 sannan ta yi sanadin hasarar dimbin dukiyoyi, lamarin da ya sa gwamnatin Nijer soma neman gudummowar abokan hulda na kasa da kasa don agaza wa wadanda bala’in ya rutsa da su.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani shirin hadin gwiwa da Bankin Duniya mai lakanin “Haske” da nufin samar da wutar lantarki da makamashi a daruruwan garuruwan kasar.
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso Paul Henri Sandaogo Damiba ya kai ziyara a Jamhuriyar Nijer da nufin neman hanyar shawo kan matsalolin da su ka addabi yankin.
A Nijr, an gudanar da bikin kaddamar da ayarin zaman lafiya inda cibiyar fina-finai ta CINE NOMADE da tallafin ofishin jakadancin Amurka a Nijar za ta zagaya jihohin kasar da nufin tattaunawa da jama’a akan batun zaman lafiya musamman matasa.
Domin Kari