A daya gefe kuma sha’anin tsaro na kara ta’azzara a wasu yankuna lamarin da ke nuna rashin tasirin matakin girke rundunar sojojin Faransa a kasar duk da cewa gwamnatin ta Nijar ce ta bukaci samun irin wannan dauki domin tunkarar kungiyoyin ta’addanci da suka addabi yankin Sahel.
Tsadar farashin kayan abinci da sauran ababen masarufi na daga cikin matsalolin da hadakar M62 ta ce hukumomin Nijar su ka yi biris a kai a wani lokacin da ake fama da karancin kudi a hannun jama’a, yayin da a wasu yankunan aika -aikar ‘yan bindiga ta hana talakawa gudanar da ayyuka a gonak,i hasali ma dubun dubutar mutane sun kauracewa garuruwansu sanadiyar tashe tashen hankula
Wannan ne kuma babban dalilin da yasa kungiyoyin suka kudiri aniyar fitowa kan titunan birnin Yamai a ranar Lahadi 30 ga wannan watan Oktoba, domin ankarar da mahukunta halin da ake ciki kamar yadda suka sanar a taron manema labarai.
Matakin girke dakarun Barkhane a Nijar bayan ficewar rundunar daga kasar Mali wani abu ne da bai dace ‘yan kasa su aminta da shi ba a cewar M62. Dalili kenan ta bukaci jama’a su hallara a wannan zanga- zanga domin nuna bukatar ficewar sojan Faransa daga Nijar duk kuwa da cewa gwamnatin kasar ce ta nuna bukatar samun dauki daga kasashe aminnai.
Sai dai alamu na nunin an samu baraka a tsakanin jagororin wannan tafiya kamar yadda Falmata Taya mai magana da yawun bangaren Abdoulaye Saidou ta bayyana. Ta ce, “Akwai wasu da ‘yan siyasa suke turo su domin su zo cikin mu su bata muna rawar mu da kura.”
A jajibirin ranar bukin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kan Nijer daga turawan mulkin mallaka ne hadakar M62 ta bada sanarwar shigowarta fagen gwagwarmaya abinda ya ba ta damar shirya zanga- zangar lumana a ranar 18 ga watan satumba a biranen Yamai da Dosso domin kalubalantar mahukunta akan matsalolin da ke da nasaba da sha’anin gudanar da mulkin kasa.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti: