Bayanai dai sun tabbatar da cewa, ba'a damawa da su wajen tafiyar da ayyuka a wannan fanni, sannan basa samun damar cin moriyar kudaden da ke shigowa kasar ta hanyar ma’adanan karkashin kasa.
Wannan shine mafarin shirya taron hadin guiwa da shugabannin mata domin nazarin hanyoyin da za a bullowa wannan batu.
A hirar shi da Muryar Amurka, Malan Iliyassou Boubakar wanda aka fi sani da sunan Shata daya daga cikin shika shikan ROTAB ya ce, "kasar Nijar ce wacce ake hako ma’adanai, akwai man fetur, zinare da karfen Uranium da dai sauransu kuma idan kuka dauka cikin kashi 100 wajen kashin 50 da wani abu duka mata ne kuma matasa kusan kashi 100 wajen kashi 70 duka matasa ne, amma binciken ya nuna cewa kamar ba a damawa da su."
Kasar Nijar tayi fice a duniya akan maganar karfen Uranium arzikin da wasu kamfanonin Faransa suka shafe shekaru sama da 40 suna hakowa kafin a shekarar 2021 a rufe daya daga cikin wadannan mahaka, saboda abinda aka kira faduwar darajar Uranium a kasuwanni.
A nata bayanin, Madame Boukari Kadidjatou daya daga cikin mahalarta wannan taro daga jihar Agadez, ta ce suna son gwamnatin ta rika tunanin matasa da ake da su, a kuma rika tunanin yadda za a tallafawa mata a bisa harkar ma’adanai, sabili da ana fama da rashin aikin yi da ya sa abubuwa suka tsaya cak.
Haka su ma matan jihar Diffa mai arzikin man fetur ke kokawa da rashin samun damar shiga a dama al’amura da su, ballantana su ci moriyar wannan arziki yau shekaru sama da 10 bayan fara sayar da man Nijar a kasuwannin ciki da wajen kasar, alhali akwai mata ma’ilmanta da ke iya taka rawar gani, in ji Madame Malami Fati daga kungiyar ROTAB reshen Diffa.
Rashin shigar da mata a harkokin gudanar da arzikin ma’adanai na daga cikin manyan dalilan da suka sa jama’a ba ta gani a kasa, sanadiyar rashin hasken da ke tattare da maganar kasafta kudaden shigar wannan fanni, kamar yadda Madame Moctar Nana Fatima Kango ta bayyana.
A karshen wannan zama na wuni 2 mahalartan zasu bullo da shawarwarin da za’a gabatar wa hukumomi don ganin an sake lale a fannin al’amuran ma’adanai a Nijar, inda a yanzu haka ake gudanar da ayyukan shimfida bututun man fetur na hadin guiwa da jamhuriyar Benin don soma fitar da shi zuwa kasuwannin duniya yayin da a daya bangare wani kamfanin kasar Canada ya kaddamar da ayyukan hakar Uranium a makon jiya a yankin arewacin kasar.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: