Masu ruwa da tsaki da wasu ‘yan Najeriya a kusan kowane bangare na bayyana mabambantan ra’ayoyi kan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da a ke kimanin mako biyu shugaban ya yi ban kwana da fadar gwamnatin kasar.
Shin wadanda su ka lashe zabe za su cika alkawarin kyautata rayuwar matasa ko sun yi zane kan ruwa ne, matasan sun duba matakan dogaro da kai maimakon jiran gawon shanu.
Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya NBC ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya da ya haramta ma ta cin tarar kafafen yada labaru da su ka saba doka.
Sabbin 'yan majalisar wakilan Najeriya sun ce za su hada kai don magance zargin da a ke yi wa majalisa na zama 'yar amshin shatan sashen zartarwa.
Hankalin 'yan Najeriya ya koma kan sauran dalibai da su ka makale a kan iyakar Sudan da Masar bayan isowar rukunin farko na 'yan Najeriya 366 sun iso gida.
Wannan kira na daga manyan bukatun da kungiyar ta gabatar a bikin ranar ma'aikata ta bana.
INEC na mayar da martani ne kan wasikar da Hudun ya rubutawa babban sufeton kan dalilansa na ayyana sakamakon zaben na jihar Adamawa.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnati na daukar matakan dawo da ‘yan Najeriya gida don kauce wa rikicin Sudan ta hanyar kasar Masar.
A lokacin gaisuwar idin karamar sallah da al’ummar Abuja da a ka canka karkashin ministan Abuja Muhammad Musa Bello zuwa fadar Aso Rock, shugaban ya nemi ahuwar jama’a a kusan shekaru 8 da ya yi ya na mulkin kasar.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta mika batun binciken kwamishinan ta na zabe a jihar Adamawa Barista Ari Hudu ga babban sufeton ‘yan sanda Baba Usman Alkali don daukar matakin doka da ya dace.
An shiga rufe tafsirin azumin watan ramadan na shekarar bana ta hijira 1444 a manyan majalisun tafsirin a sassan Najeriya daban-daban don shirin idin karamar sallah ko tafiya Saudiyya don umrah.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta dakatar da shugaban hukumar na jihar Adamawa daga shiga ofishin ko kusantar ofishin har sai an dauki mataki na gaba.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce kwamishinan zabenta a Adamawa ya yi gaggawar fadin sakamakon zabe ba tare da kammala tattara sakamakon ba.
Jihar Adamawa a arewa maso gabar da Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cikin shirin kammala zaben gwamnoninsu Asabar din nan.
Kafafen labarun Najeriya sun fara yayata sunayen wasu manyan 'yan jam'iyyar APC da a ke tallatawa don samun mukamai a gwamnatin Tinubu.
Tun da farko, wadanda suka samu umurnin kotu na dakatar da Abure sun yi dafifi a helkwatar jam’iyyar don hana shi yin jagaoranci.
Malaman Islama da addinin Kiristan nan biyu wato Imam Nuraini Ashafa da Pastor James Wuye sun nuna cewa hadin kan jama’a ta hanyar kauce wa bambance-bambance ne zai dawo da Najeriya kan turba mai kyau ta zaman lafiya.
Domin Kari