Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Majalisun Tafsiri Yayin Da Ramadan Ya Zo Karshe


Dr. Muhammad Kabir Hauruna Gombe A Taron Rufe Tafsiri A Masallacin JIBWIS Na Utako Da Ke Abuja
Dr. Muhammad Kabir Hauruna Gombe A Taron Rufe Tafsiri A Masallacin JIBWIS Na Utako Da Ke Abuja

An shiga rufe tafsirin azumin watan ramadan na shekarar bana ta hijira 1444 a manyan majalisun tafsirin a sassan Najeriya daban-daban don shirin idin karamar sallah ko tafiya Saudiyya don umrah.

A na sa ran gudanar da idin na karamar sallah na bana ranar Jumma'ar nan ko Asabar mai zuwa wato 21 ko 22 ga watan nan na Afrilu.

A helkwatar JIBWIS da ke Utako Abuja, Dr. Muhammad Kabir Hauruna Gombe ya rufe tafsirin da jan hankalin duk wanda Allah ya ba wa jagoranci musamman irin na dimokradiyya ya sani akwai wa'adin kammala mulkin.

Shehun malamin ya ce abun da zai taimakawa jagororin shi ne wasu shugabannin da su ka shude.

Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja
Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja

Hakanan malamin ya bayyana shirin JIBWIS na daukar nauyin marayu mata masu kwazon karatu a lokacin auren su.

Mai martaa Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Musa Ijakoro ya halarci rufe tafsirin a madadin sarakunan yankin birnin tarayya Abuja.

Taron Rufe Tafsirin Al'qurani A Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja
Taron Rufe Tafsirin Al'qurani A Masallacin Helkwatar JIBWIS Da Ke Utako Abuja

An ga mutane na nuna juyayin karatowar karshen azumin da kan kasance wata da mutane kan kara kaucewa miyagun aiyuka yayin da wasu masu hannu da shuni kan kyautatawa sauran talakawa.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG