Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya 366 Sun Isa Abuja Daga Sudan


Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan
Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan

Hankalin 'yan Najeriya ya koma kan sauran dalibai da su ka makale a kan iyakar Sudan da Masar bayan isowar rukunin farko na 'yan Najeriya 366 sun iso gida.

Gwamnatin Najeriya ta kwaso rukunin farkon ne bayan cikas da aka samu a farko sakamakon hana 'yan kasashen ketare ketara kan iyaka da kasar Misira ta yi da farko ba tare da takar izinin shiga kasa ta bisa ba.

Mutanen da aka kwaso a rukunin na farko ya hada da sauran dalibai da ‘yan Najeriya da su ka bi ta kasashen da su ka hada da Habasha da Saudiyya.

Dawowar daliban a jirgin kamfanin AIR PEACE ya kawo farin ciki a zuciyar iyaye da ke kwana cikin fargaba don barkewar fitinar Sudan a ranar 15 ga watan jiya.

Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan
Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan

Tsaikon da jigilar ya samu na amfani da motoci da su ka ratsa Sahara zuwa Masar ya kawo cece-kuce da bukatar kara daukar matakai don tsaron lafiyar daliban.

Dangane da matsayin dimbin daliban da su ke kan iyaka kuma rahotanni ke nuna ba su samu damar shiga kasar Masar ba, Ministar jinkai Sadiya Umar ta ce za a cigaba da jigilar kasancewa, ba zai yiwu a kwaso kowa a lokaci daya ba.

Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan
Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan

Dangane kuma da kokawa da dalibai da ke a kan iyaka ke yi na rashin samun abinci ko kulawar da ta dace, Ministar ta bayyana cewa, ana daukar duk matakan kulawa da daliban.

A hira da wadansu dalibai da Muryar Amurka ta yi, sun bayyana irin halin kunci da suke ciki da ya hada da rashin abinci da kuma yanayi mai inganci.

Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan
Dawowar 'Rukunin Farko Na Yan Najeriya Daga Sudan

Jirgin soja da na AIR PEACE sun iso da adadin mutum 366.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG