ABUJA- Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC da TUC ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kara wa'adin ritaya daga aiki zuwa shekaru 65 na rayuwa da kuma 40 na aiki.
Wannan na daga manyan bukatun da kungiyar ta gabatar a bikin ranar ma'aikata ta bana.
A tsarin aiki a Najeriya dai ma'aikaci zai yi ritaya in ya kai shekaru 60 na rayuwa ko kuma daga fara aiki ya kai shekaru 35 da hakan kan sa ganin ma'aikaci da sauran kuzarinsa amma dole ya ajiye aiki.
Shugaban kungiyar ma'aikatan kamfanoni TUC Komred Festus Osifo da ke magana gefe da shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero ya bukaci gwamnatin ta kara shekaru 5 ga kowane bangaren mai ritaya kamar yanda ta yi wa wasu sassan aikin gwamnati.
Osifo ya nuna takaicin yanda a ke samun matsalar rashin samun kudin ajiye aiki "gratutity" da ma'aikaci kan yi amfani da su wajen sayan gida ko samun jari bayan ritaya. Hakanan fansho ma bai taka kara ya karya ba.
Tsohon ma'aikacin gwamnatin tarayya Fred Manjack na daga 'yan fansho da ke dagewa a gyara tsarin da tsame hannayen wasu mafanonin da ya zaiyana da na 'yan jari hujja daga kula da kudin tsoffin ma'aikatan.
Baya ga Manjack wanda ya ce kamfen din sa ya isa kunnen gwamnati da samun 'yar sa'ida, wani ma'aiakcin ilimi da ya samu karin shekaru 5 bayan ritaya ya ce kudin sa sun makale da wasu 'yan rukunin aikin su.
Najeriya dai na daga cikin kasashen da mafi karancin albashi ba zai iya sayen rabin buhun shinkafa a wasu jihohin ba; inda a wasu kuma sai an samu ciko kafin samun buhun.
Rashin samun fansho da giratuti mai kyau kan sa wasu ma'aikatan shiga yanayin dimuwar kai, yawan rabkanuwa da neman bashi.