Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce ba ruwanta da wasikar kare kai da kwamishinanta na Adamawa Barista Ari Yunusa Hudu don ta umurci shi ne ya mika kansa ga babban sufeton ‘yan sanda don gudanar da bincike kan ayyana sakamakon zaben Adamawa ba da hurumi ba.
INEC na martani ne kan wasikar da Hudun ya rubutawa babban sufeton da tura ma ta kofi kan dalilansa na ayyana sakamakon zaben.
Hukumar wacce da ma ta dakatar da Hudu bayan ayyana Sanata Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zabe, ta bukaci rundunar ‘yan sanda ta gudanar da bincike kan abubuwan da su ka faru don daukar matakan shari’a.
Jami’a a sashen labarun hukumar, Zainab Aminu, ta ce INEC ba za ta karbi ko duba wani sako daga kwamishinan da a ka dakatar ba sai in an samu sakamakon binciken.
Hudu Ari dai ya yi zargin babban baturen zaben da dan rakiya ya gana da gwamnan Adamawa Umar Fintiri a gidan gwamnati don haka yaga ba za’a samu adalci ba; don haka ya sanar da sakamakon da ya ce yana da yakinin gaskiyar sakamkon zaben ke nan.
In za'a tuna gwamna Fintiri da ya ke karbar shaidar lashe zabe ya yi alwashin daukar matakin shari’a kan kwamishinan.
A na su bangare magoya bayan ‘yar takarar APC Aisha Binani da bayanai ke nuna ta shirya garzayawa kotu, sun ce za su kalubalanci gwamna Fintiri kan sakamakon zaben.
Umar Garkuwa na kan gaba a masu hamaiya da Fintiri ya ce za su bi duk hanyoyin shari’a don neman dawo mu su da nasara.
Baya ga zantawa da wasikar da Hudu ya aikawa hukumomi, za a iya cewa ya na wani waje da ba a sani ba kuma rundunar ‘yan sanda ba ta aiyana neman sa ruwa a jallo ba.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: