ABUJA, NIGERIA - Shugaban hukumar agajin Mustapha Habib wanda ke birnin Alkahira na Masar ya ce za a gudanar da jigilar ta hanyar motoci don kauce wa hatsarin amfani da filin jirgin sama a Khartoum.
Bayanin dai ya nuna Najeriya za ta yi shatar motoci don jigilar dalibai da sauran 'yan kasa da ke makale a Khartoum cikin fargaba.
Mustapha Habib ya ce su na bin aikin cikin takatsantsan don wasu da ba 'yan kasa ba ka iya bin tawagar ta ‘yan Najeriya.
Ita dai fitinar da ta hada da shugaban gwamnatin soja na Sudan Janar Abdelfatah Burhan da krma na 'yan ko-ta-kwana Janar Hamdan Dagalo ta na da alaka da yanda tsohon shugaba Janar Omar Elbashir ya maida tsoffin mayakan JANJAWEED a Darfur da Dagalo ke jagoranta zuwa tamkar sashen sojan kasar.
Mai sharhi kan Sudan wanda ya yi karatu a Khartoum, Barista Auwal Abdulkadir Albarudi, ya ce tsama ce tsakanin sassan biyu ta mamaye madafun iko.
Hakika har dai tsagaita wuta a Sudan bai dore ba, fitinar za ta ci gaba da zama ruwan dare don Sudan na daga cikin kasashen Afirka da ke da mazauna daga kusan dukkan nahiyar.
Sauarari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya: