Sunayen sun hada da na gwamnoni da ke kammala wa'adi na karshe da za su sauka daga mulki a watan gobe.
Kazalika akwai sunayen wasu da su ka taka rawa a bangarori daban-daban na kamfen din Tinubun da su ma a ka rubuta sunayen su da tunanin za su samu mukamin minista.
Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr. Farouk BB Farouk ke dauko tanadin tsarin mulki da ya ba wa shugaba hurumin canko wadanda ya ga zai iya aiki da su.
Shin akwai alamun Tinubu zai sauya salo daga na shugaba Buhari da kan nada mukamai ba tare da tuntubar gwamnoni ko ‘yan jam’iyya a jiha ba?
Dattuwa Ali Kumo dan kwamitin gudanarwa na APC ne da ke cewa wannan karo duk wanda ya yi dawainiya zai samu gurbi a gwamnatin.
Shi ma shaharerren dan siyasa a Abuja Musa Dala na fatan Tinubu ya koma irin tsarin PDP na mutunta wadanda su ka yi wa jam’iyya dawainiya.
Dr.BB Farouk a nan ya yi nazarin daga arewa ba za a samu sauyi na cigaba da kashin dankalin ‘yan jari hujja ba, amma a kudu za a iya fakewa da kwarewa wajen cankar wadanda a ke so.
A sabuwar doka da shugaba Buhari ya rantabawa hannu, sabon shugaba zai fito da sunayen wadanda zai nada a majalisar ta zartarwa cikin kwana 60 bayan hawa karagar mulki.
Ga sautin rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: