Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC ta Dakatar Da Shugaban Hukumar Na Adamawa Daga Shiga Ofis


Hukumar INEC
Hukumar INEC

Hukumar zaben Najeriya INEC ta dakatar da shugaban hukumar na jihar Adamawa daga shiga ofishin ko kusantar ofishin har sai an dauki mataki na gaba.

Wannan na cikin matakan da Hukumar ta dauka biyo bayan dakatar da ayyana sakamakon zaben gwamnan Adamawa.

A wata takarda dauke da sa hannun hukumar Rose Oriaran Anthony ta umurci kwamishinan zaben Barista Hudu Yunusa Ari ya dakata daga aikin sa kazalika sakataren mulki na ofishin ya karbi madafun iko.

Matakin dai inji Anthony ya fara aiki ne nan take.

Jami’a a sashen labaru ta hukumar Zainab Aminu ta yi karin bayani kan matakin yayin da hukumar ke cigaba da ganawa da sauran masu ruwa da tsaki.

A na sa ran komawa Adamawa don cigaba da tattara sakamakon zaben daga talatar nan a yayin da bangaren APC da PDP ke fatar samun nasara.

Aisha Binani ta APC na kalubalantar gwamnan Adamawa Umar Fintiri a zaben gwamnan na Adamawa da a ka samu kalubalen tattarawa da aiyana sakamakon.

A Saurari Sautin Nasiru Adamu El-Hikaya:

ZAINAB AMINU CLIP ON HUDU ARI.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG