Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Karfafa Zaman Tare Fiye Da Bambance-Bambance – Malaman Addini


Nuraini Ashafa da Mover Wuye
Nuraini Ashafa da Mover Wuye

Malaman Islama da addinin Kiristan nan biyu wato Imam Nuraini Ashafa da Pastor James Wuye sun nuna cewa hadin kan jama’a ta hanyar kauce wa bambance-bambance ne zai dawo da Najeriya kan turba mai kyau ta zaman lafiya.

Jami’an addinan biyu na magana ne a shirye-shiryen da su ke jagoranta na kawo fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista da wasunsu, su ka samu sabani sanadiyyar lamuran siyasa.

Nuraini Ashafa da Movel Wuye wadanda su ka taba samun raunuka sanadiyyar rikicin addini sun ce bisa ga tanadin tsarin mulki, kowa ya na iya bin addinin da ya ga zai fishsheshi ba tare da samun tsangwama ba.

Sheikh Ashafa ya ce matukar za a rika zama tare to za a iya samun maslaha ga kowace irin fitina ko kiyayya a tsakanin jama’a.

A nasa bangare, Pastor Movel Wuye, ya ce ta hanyar dabi’u masu kyau da kyautatawa tsakanin mabiya addinai za a samu fahimtar juna da zaman da ya sabawa na doya da manja.

Wasu malaman addini a bangaren Musulmi da Kirista na amfani da damar bayan babban zaben Najeriya wajen jan hankalin mabiya addinan da ko sun yi zabe bisa shaukin addini, to yanzu lokacin ci gaba da zaman tare ne a kasa daya mai addinai, kabilu daban-daban da ra’ayoyi da kan ci karo da juna.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG