Za a maimaita zaben a wasu mazabu a jihohin biyu don samar da wanda ya yi zarra don aiyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wasu jihohin kuma kamar Kano, Zamfara da Sokoto akwai maimaita zaben wasu ko duk kujerun majalisar dattawa da wakilai.
Hukumar zaben INEC ta ce ta na shirye tsaf don gudanar da kammala zaben.
Zainab Aminu jami’a ce a sashen labaru ta hukumar da ke cewa duk shirye-shirye sun kammala don zaben.
Maimaita zaben jihar Adamawa ya fi daukar hankalin kasa don kasancewar ‘yar takara mace Aisha Binani a APC ke kalubalantar gwamnan jihar Umar Fintiri da ke neman tazarce karo na biyu.
Dattijon siyasar NEPU Hussaini Gariko ya ce zaben na 2023 ya zama babban darasi a Najeriya amma duk da bai kawo sauyin tsarin masu takarar zaben ba daga muradun lashe zabe kadai maimakon zama wakilan jama’a na hakika.
Hakanan Gariko ya ce yayin da gwamnati mai ci kan dage don samun karin jihohi, ‘yan adawa kuma sai sun koyi kulla kawance matukar su na son nasara kamar yanda jam’iyyu su ka narke gabanin 2015 su ka zama APC.
Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Abuja, Dr. Farouk BB Farouk, ya ce ‘yan adawa musamman babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta gaza komawa can kasa wajen talakawa kamar yanda shugaba Buhari ya dinga yi har ya dare madafun iko.
Duk jam’iyyar da ta lashe zabe ranar asabar, zai kara ma ta tagomashi a lamuran taraiya da ma farautar wasu jiga-jigai daga wasu jam’iyyun don zaben 2027.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: