A kalla 'yan kabilar Kambari dubu biyar ne suka halarci taron su na wannnan shekarar, duk da matasalar da yankin nasu yake fama da shi na rashin hanyar motada sauran ababan more rayuwa.
Hukumar Kula da kare Hakkin Mata da yara kanana a jihar Nejan Nigeria tace ta fara gudanar da bincike akan auren wani Dattijo Dan Kimanin Shekaru 61 Mai suna Alhaji Yakubu Umar Mainasara dake Zaune a garin Lapai da kuma wata yarinya da aka ce tana da karancin Shekaru.
Daruruwan tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar Nejan Nigeria ne sun yi dafifi a harabar ofishin hukumar fansho ta jihar domin karbar kudadensu na sallama daga aiki da hukumar kula da kudaden fanshon ta fara biya a ranar Litinin goma ga watan Disamban 2018.
Gwamnan Jijhar Neja Abubakar Sani Bello yace yana nazari akan sabon tsarin albashi na naira dubu 30 da aka cimma yarjejeniya a tsakanin kungiyar kwadagon Nigeria da kuma gwamnatin Kasar,
Malamai da ma’aikatan Makarantun gaba da sankandire a Jihar Neja sun tsunduma yajin aikin har sai abinda hali yayi daga yau alhamis, bayan yajin aikin gargadi da suka shiga mako guda da ya gabata.
Bankin Duniya ya bayar da tallafin kudi, dalar Amurka Miliyan biyu domin fara aikin gyara wuraren da zaizayar kasa ta shafa sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta bana a jihar Neja dake Arewacin Nigeria.
Gwamna jihar Neja a Najeriya Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce ya zama tilas shugabannin siyasa su dauki matakin shawo kan kisan jama’a da yaki ci yaki cinyewa a jihar Filato dake Arewacin kasar.
Daruruwan masu zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Neja sun rufe babbar hanyar motar da ta hada Minna zuwa sokoto da Birnin Kebbi da kuma Kontagora.
Masu ruwa da tsaki a Nigeria na ci gaba da yin tsokaci akan labarin da ya fito a kafofin yadda labarai cewar tsohon gwamnan jihar Pilato Joshua Dariye dake zaman daurin shekaru 14 a gidan kaso ya yanki fom din tsaya takarar neman mukamin sanata a majalisar dattawan Najeriya a karkashin innuwar jam’iyyar APC mai mulki.
Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya ta fara wayar da kan matasan Fulani a kan illar shaye-shayen kayan maye da bangar siyasa.
Sakamakon ambaliyar da ruwa da aka samu sama da kadada dubu 75 na gonakin shinkafa ne suka lalace a jihar Neja, dake arewacin Najeriya.
Majalisar Dokokin jihar Neja a Nigeria ta kori daya daga cikin mambobinta, Hon. Danladi Iya, mai Wakiltar karamar Hukumar Tafa.
Jakadan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu ambasada Ahmad Musa Ibeto ya yi murabus daga aiki, sannan ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki a ya koma jam’iyar adawa ta PDP.
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya ce sama da kashi 60 na malaman makarantu a jihar basu da ilimin koyarwa a makarantun.
Kungiyar manoman jihar Neja ta ce ta damu da rashin hukunta masu saida takin zamani na jabu to amma Gwamnatin Nejan ta ce ta dauki mataki kuma yanzu ma babu jabun takin a jihar.
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewar tana tabka asarar kudi kimanin Naira miliyan 200 a duk kowane karshen wata a sakamakon Ma’aikatan Bogi da sukayi katutu a jihar.
Bankin Duniya zai kashe Dalar Amurka Milyan 60 wajan gyara Hanyoyin karkara a jihar Neja.
Domin Kari