Kungiyar manoman jihar Neja ta ce ta damu da rashin hukunta masu saida takin zamani na jabu to amma Gwamnatin Nejan ta ce ta dauki mataki kuma yanzu ma babu jabun takin a jihar.
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewar tana tabka asarar kudi kimanin Naira miliyan 200 a duk kowane karshen wata a sakamakon Ma’aikatan Bogi da sukayi katutu a jihar.
Bankin Duniya zai kashe Dalar Amurka Milyan 60 wajan gyara Hanyoyin karkara a jihar Neja.
Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ta Najeriya ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin APC ke tafiyar sha’anin mulkin kasar.
Gwamnatin Najeriya tace ta dukufa wajen shawo kan matsalar zaizayar kasa dake barazana a sassa daban daban a fadin kasar.
Hukumomin jihar Kwara sun yi alkawarin ba da ladan Naira miliyan biyar ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga cafke wasu 'yan fashi da suka kai hari wasu bankuna, har suka kashe mutane da dama a garin Offa.
Sanadiyyar rashin biyansu wasu alawus alawus da rashin samar musu da kayan aiki kamar motoci, musamman a kotunan majistare da na shari'a suka sa alkalan rubutawa gwamnati wasikar shirin zuwa yajin aiki idan ba'a biya masu bukatunsu ba nan da kwanaki 20
Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kare matsayin da gwamnonin APC suka dauka na nuna bukatar ganin shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsaya wa takara a zaben 2019.
Taron Alarammomin Najeriya reshen jihar Neja ya yi tur da ayyukan kungiyar Boko Haram bisa cewa addinin Musulunci bai koyar da muggan ayyukan da kungiyar ke aikatawa ba, tare da shan alwashin taimakawa wurin fadakar da jama'a
Wasu kungiyoyin fararen hula da suka hada da mabiya addinin Musulunci da na Kiristanci suka taru a Minna babban birnin jihar Neja domin gudanar da addu'oin rokon Allah Ya sa a sako sauran 'yan matan Chibok da sabbin da aka sace a makarantar sakandare ta mata dake garin Dapchi, jihar Yobe
Biyo bayan sace 'yan matan makarantar sakandare ta Dapchi dake jihar Yobe da wadanda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi, yanzu rundunar sojojin Najeriya ta kuduri aniyar sa ido a kan duk makarantun sakandare na mata dake yankin arewa maso gabashin kasar
Sarki Sanusi na Biyu ya bukaci shugabannin makiyayan da su tabbatar duk lokacin da aka gayyace su taro, sun fadawa manyan sarakuna don tabbatar da cewa an tura wanda zai iya kare muradunsu.
Hukumomin lafiya a jihar sun ce ana sa ran yin rigakafin kamuwa da wannan mummunar cuta ga yara kimanin miliyan daya wadanda suka kama daga masu watanni tara da haihuwa har zuwa shekaru biyar