Kimanin mutane 40 ne suka rasa rayukan su a jihar Neja dake Arewacin Najeriya, sakamakon ambaliyar da aka samu da ta samo asali daga ruwan sama da akayi kamar da bakin kwariya a yankin.
Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, yayi wata ziyarar gani da ido ta jirgin sama mai saukar angulu domin duba irin barnar da ambaliyar tayi.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar ya shaida cewa ana ci gaba da lissafa mutanen da suka rasu, ya kuma kara da cewa kauyaku sunfi 200 da ruwan yayi awon gaba da su.
Saurari Rahoton Mustapha Nasiru Batsari....
Facebook Forum