Ambaliyar ruwan ta shafi kimanin kananan hukumomi 17, inda hukumomin jihar suka ce ambaliyar ta faru ne sakamakon tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi, da kuma bude madatsun ruwa na Shuroro da Kayinji da kuma Jaba.
Shugaban kungiyar manoman shinkafa na jihar Alhaji Muhammadu Sani, ya ce suna cikin wani yanayi na tashin hankalin, kasancewar an wayi gari sama da manoman shinkafa dubu 25 sun yi asarar kayan amfanin gonakinsu saboda ambaliyar ruwan da ta faru.
A ta bakin kwamishinan ma’aikatar gona, Alhaji Nuhu Haruna Dukku, ya ce gwamnatin jihar Neja ta ce ta kafa wani kwamniti da zai tantance barnar da aka samu, domin taimakawa manoman.
A wani labarin kuma, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Neja, Alhaji Ibrahim Inga, ya tabbatar da samun hatsarin wani jirgin ruwan kwale-kwale a kan rafin Shiroro, inda ake fargabar cewa mutane tara sun bace.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum